Yadda aka je har gida, aka maƙure babban ‘Dan Sanata Na Allah inji Gwamnatin Kaduna

Yadda aka je har gida, aka maƙure babban ‘Dan Sanata Na Allah inji Gwamnatin Kaduna

  • Kisan Abdulkarim Bala Na’Allah ya sa Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da jawabi
  • Samuel Aruwan yace wasu ne suka shiga gida, suka kashe wannan Bawan Allah
  • Gwamna Nasir El-Rufai ya aika ta’aziyya, ya kuma nemi jami’an tsaro suyi bincike

Kaduna - Rahoton da Daily Trust ta fitar, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna ta yi magana a game da mutuwar ‘dan Sanata Bala Ibn Na’Allah.

Gwamnatin Kaduna ta ce wani ne ya kashe Kyaftin Abdulkarim Na’Allah ta hanyar shake masa wuya.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar da jawabi, yace jami’an tsaro sun sanar da su game da mutuwar.

Da yake jawabi a yammacin Lahadi, Samuel Aruwan yace mutuwar ta yi kama da kisan-kai, inda aka makure marigayin da igiya, har yace ga garinku nan.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

Abin da Samuel Aruwan ya fada

“A abin da yake kama da kisan-kai, an tsinci gawar marigayin ne a cikin dakin kwanansa a gidansa da ke Malali, karamar hukumar Kaduna ta Arewa.”
“Bayan an shake shi da igiya, an kuma sace wata mota da ta ke ajiye a cikin gidan marigayin.”

Babban ‘Dan Sanata Na Allah inji Gwamnatin Kaduna
Kyaftin Abdulkarim-NaAllah Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Menene matakin da Gwamna ya dauka?

“Gwamna Nasir El-Rufai ya ji takaicin samun wannan rahoto, ya kuma roki Ubangiji ya yi wa marigayin rahama, ya aika ta’aziyyarsa ga danginsa."
“Mai girma gwamna ya yi kira ga jami’an tsaro su gudanar da kwakkwaran bincike domin a bankado wadanda suka yi wannan aiki, a hukunta su.”

Mai girma Kwamishinan ya bada tabbacin cewa tuni dai jami’an tsaro suka fara binciken lamarin. Jaridar PM News ta kawo wannan rahoton dazu.

Kara karanta wannan

Bauchi: 'Yan sanda sun yi ram da mutum 352 da ake zargi da garkuwa da mutane

Ba 'yan bindiga ba ne

Wannan ikirari da gwamnatin ta yi a ranar Lahadi, 29 ga watan Agusta, 2021, ya saba wa rahoton da aka ji na cewa ‘yan bindiga ne suka kashe Na’Allah.

Jihar Kaduna na cikin inda ake fama da matsalar ‘yan bindiga a Arewacin Najeriya, amma gwamnati ta nuna ba ‘yan bindigan ne suka yi wannan ba.

Mahaifin marigayin shi ne Sanata mai wakiltar kudancin Kebbi a majalisar dattawa, ya na da ‘ya ‘ya maza uku a Duniya, dukkansu matukan jirgin sama ne.

Jaridar ta ce an kashe Kyaftin Na’Allah mai shekara 36 ba da dade wa da yin aure ba. Sai da aka daure shi, aka kakara masa igiya, har ya daina numfashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel