Jigawa: Ɗalibai 10 Sun Kutsa Gidan Wani Mutum Cikin Dare Sun Ɗaure Shi Sun Masa Askin Dole

Jigawa: Ɗalibai 10 Sun Kutsa Gidan Wani Mutum Cikin Dare Sun Ɗaure Shi Sun Masa Askin Dole

  • Wasu dalibai 10 sun kutsa gidan wani mutum cikin dare sun masa askin dole a Jigawa
  • Rundunar yan sanda ta ce ta yi nasarar kama shida cikin daliban 10 bayan mutumin ya yi korafi
  • Kakakin yan sandan Jihar Jigawa, ASP Shiisu ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu idan an gama bincike

Rundunar yan sanda a Jihar Jigawa ta kama wasu dalibai shida da suka kutsa gidan wani mutum suka aske masa gashin kansa karfi da yaji, News Wire NGR ta ruwaito.

Ana kan neman wasu karin mutane hudu da ake zargin yayin da tuni yan sandan sun bazama nemansu don kama su.

Jigawa: Ɗalibai 10 Sun Kutsa Gidan Wani Mutum Cikin Dare Sun Ɗaure Shi Sun Masa Askin Dole
Taswirar Jihar Jigawa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jigawa, ASP Lawan Shiisu, ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai da ya yi a Dutse a ranar Talata kamar yadda News Wire NGR ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

A cewar Shiisu, sun kutsa gidan wanda abin ya faru da shi a ranar 20 ga watan Agusta misalin karfe 1 na dare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanda abin ya faru da shi mai suna Ibrahim Sambo mazaunin unguwar Yalwawa Quaters a Dutse ya kai korafi ofishin yan sanda a ranar 27 ga watan Agusta.

An ce daliban suna karatu ne a 'Jami'ar Tarayya ta Dutse da Kwalejin Fasaha ta Jigawa, Dutse.'

Kakakin yan sandan ya ce wanda ya shigar da korafin ya kuma ce ya fara rashin lafiya kwanaki biyu bayan afkuwar lamarin.

Shiisu ya ce:

"A ranar 27 ga watan Agusta misalin karfe 4 na yamma, wani Ibrahim Sambo mazaunin Yalwawa Quaters, Dutse, ya yi korafin cewa a ranar 20 ga watan Agusta misalin karfe 1 na dare, wasu daliban Jami'ar Tarayya ta Dutse da Jigawa Polyteknik, Dutse, sun kutsa gidansa, sun daure shi suka yi masa aski na dole suka tafi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan sanda sun yi nasarar kasha Shugaban IPOB/ESN a kudu maso gabas

"Bayan kwanaki biyu ya fara rashin lafiya."

An yi nasarar kama shida cikin daliban

Kakakin ya kara da cewa bayan samun korafin, yan sanda sun kamo shida cikin daliban masu shekaru 18 zuwa 19 da ake zargi da laifin.

Ya ce:

"Wadanda ake zargin, da sun amsa laifin za su gurfana a kotu da zarar an kammala bincike."

Jigawa: Hotunan Auren Yaya Da Ƙanwa da Kotun Shari’ar Musulunci Ta Aurar da Su Duk da Ƙin Amincewar Mahaifinsu

A wani labarin daban, wata babban kotun Shari'a a ƙaramar hukumar Hadejia na Jihar Jigawa, a ranar Alhamis, ta aurar da wasu mata biyu ƴaƴa da ƙanwa, Premium Times ta ruwaito.

An aurar da matar biyu ne bayan mahaifinsu, Abdullahi Malammmadori, ya ƙi aurar da su duk da wa'adin kwanaki 30 da kotun ta bashi amma bai aurar da su ba.

Shugaban wata gidauniya na taimakon mata, marayu da marasa galihu, Fatima Kailanini, ta yi ƙarar Mr Malammadori kan ƙin aurar da Khadijat da Hafsat Abdullahi duk da sun fito da waɗanda suke so.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel