Babbar Magana: Jami'ai Sun Cafke Wani Bawan Allah da Ya Ɗirkawa Ɗiyarsa Ciki Har Ta Haihu

Babbar Magana: Jami'ai Sun Cafke Wani Bawan Allah da Ya Ɗirkawa Ɗiyarsa Ciki Har Ta Haihu

  • Yan bijilanti sun damke wani mutumi da ake zargin ya kwanta da ɗiyarsa har ta samu juna biyu kuma ta haife shi a Delta
  • Mutumin mai suna Akpokpokpo, ya amsa laifinsa amma yace sau ɗaya ya taba kwanciya da yarinyar kuma giya ya sha
  • A halin yanzun yan bijilanti na cigaba da bincikar mutumin inda ya amsa cewa jaririn da ɗiyar tasa ta haifa ɗansa ne

Delta - Jami'an tsaron sa kai wato yan bijilanti dake yankin Amukpe, karamar hukumar Sapele, jihar Delta, sun cafke wani mutumi mai suna Akpokpokpo, da zargin ɗirkawa ɗiyarsa ciki.

Yan bijilantin suna zargin Akpokpokpo da cewa shine mahaifin jariri ɗan wata uku da diyarsa ke ɗauke da shi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Wanda ake zargin ya keta haddin 'yarsa da ya haifa mai suna Mercy Akpokpokpo, wanda yayi sanadiyyar samun juna biyu har ta haife shi.

Kara karanta wannan

Fusatattun Direbobin Keke Nafef Sun Shiga Yajin aiki, Sun Toshe Hanyoyi a Wata Jihar Arewa

An kama wani mutumi yayi wa yarsa ciki a Delta
Babbar Magana: Jami'ai Sun Cafke Wani Bawan Allah da Ya Ɗirkawa Ɗiyarsa Ciki Har Ta Haihu Hoto: daylightng.com
Asali: UGC

Mutumin da ake zargin ya yi barazanar kashe ɗiyar tasa matukar ta fallasa sirrin abinda ya wakana tsakanin shi da ita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai yarinyar ta kasa jure wannan abun kunyar, inda ta kai rahoto ga kungiyar yan bijilanti na Amukpe, ranar 27 ga watan Augusta, 2021.

Sau ɗaya na kwanta da ita

Punch ta gano cewa bayan samun wannan rahoton ne jami'an suka tafi kai tsaye suka kame Akpokpokpo domin ya amsa tambayoyi.

Wata majiya mai karfi, tace:

"Yayin da aka tsananta bincike mutumin ya amince ya kwanta da ɗiyar tasa sau ɗaya, kuma ranar giyar da ya sha ce ta ɗibe shi ya aikata haka."
"Amma ita yarinyar ta tabbatar da cewa sau huɗu mahaifinta ya kwanta da ita. Hakanan kuma wanda ake zargin ya amince jaririn ɗansa ne."

Duk kokarin da aka yi na samun muƙaddashin kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya ci tura, domin ya yi tsokaci kan lamarin.

Kara karanta wannan

'Diyar Wani Jami'in Tsaro Ta Kai Karar Mahaifinta Bisa Keta Mata Haddi Na Tsawon Shekaru a Kano

A wani labarin kuma kunji cewa Sabuwar Kungiyar Yan Bindiga Ta Bulla a Yankin Kudu Maso Gabas

Wata sabuwar ƙungiyar yan bindiga mai suna 'Biafran Motherland Warrior’, ta bayyana yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Rahoto ya nuna cewa sabuwar ƙungiyar ta fi sojin ESN na haramtacciyar ƙungiyar yan aware IPOB hatsari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: