Ministan Buhari Ya Bukaci Hukumar EFCC Ta Fara Bibiyar Gwamna Mai Ci Kan Badakalar Wasu Kudade

Ministan Buhari Ya Bukaci Hukumar EFCC Ta Fara Bibiyar Gwamna Mai Ci Kan Badakalar Wasu Kudade

  • Ministan ayyuka na musamman, kuma tsohon gwamnan Benuwai, Akume, ya yi kira ga EFCC ta binciki Ortom
  • Ministan ya kuma bukaci gwamna Ortom na jihar Benuwai ya fito ya baiwa shugaba Buhari hakuri
  • Sanata George Akume ya yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai da ya samu halartar kusoshin APC a Benuwai

Abuja - Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akume, ya bukaci hukumar yaki da cin hanci EFCC ta fara bincikar gwamnan Benuwai, Samuel Ortom.

Sanata Akume, wanda tsohon gwamnan Benuwai ne, ya yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai a Abuja, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ministan ayyuka na musamman, Sanata George Akume
Ministan Buhari Ya Bukaci Hukumar EFCC Ta Fara Bibiyar Gwamna Mai Ci Kan Badakalar Wasu Kudade Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ministan yace:

"Muna kira ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa EFCC da ICPC su tsananta bincike kan yadda akai da kasafin kuɗin tarayya na jihar Benuwai tun daga 29 ga watan Mayu 2015 zuwa yanzu."

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya kamata gwamnatin tarayya cikin gaggawa ta bada umarnin dakatar da kason tsare dabbobi na jihar Benuwai bisa hannun gwamnatin jihar wajen aikata manyan laifuka."
"Wanda hakan ke haddasa rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali ga mazauna jihar da ba su ji ba kuma basu gani ba."

Gwamna Ortom ya baiwa Buhari hakuri

Hakanan kuma ministan ya nemi gwamna Samuel Ortom ya fito ya baiwa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, hakuri kuma ya dakatar da sukar da yake masa.

Gwamna Ortom ya jima yana takun saka da fadar shugaban ƙasa kan rikici tsakanin fulani da makiyaya da kuma matsalar tsaron da ta addabi jihar.

Akume yace:

"Muna kira ga gwamna Samuel Ortom ya baiwa shugaba Buhari hakuri saboda amfani da kalaman da ba su dace ba, da kuma shiga harkokin da basu shafe shi ba tsakanin jiha da gwamnatin tarayya."

Kara karanta wannan

Idan Bamu Yi Dagaske Ba Wataran Abujan da Muke Takama Ba Zata Zaunu Ba, Ministan Buhari

Legit.ng Hausa ta gano cewa taron manema labaran ya samu halartar kusoshi da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC reshen jihar Benuwai.

A wani labarin kuma Fusatattun Direbobin Keke Nafef Sun Shiga Yajin aiki, Sun Toshe Hanyoyi a Jihar Arewa

Masu keke nafef sun tsunduna yajin aikin gargaɗi a Minna, jihar Neja bisa matsin lambar da hukumomi ke musu.

Direbobin sun ce suna shan matsin lamba daga yan sanda, jami'an amsar haraji, jami'an VIO da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel