'Diyar Wani Jami'in Tsaro Ta Kai Karar Mahaifinta Bisa Keta Mata Haddi Na Tsawon Shekaru a Kano

'Diyar Wani Jami'in Tsaro Ta Kai Karar Mahaifinta Bisa Keta Mata Haddi Na Tsawon Shekaru a Kano

  • Hukumar kare hakkin ɗan adam ta kasa ta fara bincike kan korafin da aka shigar mata na wani mahifin mata uku
  • Ɗaya daga cikin ƴaƴansa ne ta kai rahoton cin mutunci da keta hadɗin da mahaifinsu ke musu
  • Hakanan wata mata ta ɗaure ɗan ta mai shekara 13 a gida saboda ba shi da lafiƴar kwakwalwa

Kano - Hukumar kare hakkin ɗan adam ta ƙasa (NHRC) reshen jihar Kano, tace ta fara bincike kan wani uba da ake zargin yana lalata da ƴaƴansa mata biyu, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Shugaban hukumar reshen jihar Kano, Alhaji Shehu Abdullahi, yace yarinyar yar kimanin shekara 17 ce ta kawo korafi kan mahaifin na ta.

A cewarta mahaifinsu ya jima yana keta musu haddi kusan shekara 7 kuma ba ita kaɗai ba da kanwarta yar shekara 12.

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 30, Jihar Mu Ta Fi Kowace Jiha Zaman Lafiya a Najeriya, Gwamna

Hukumar NHRC
'Diyar Wani Jami'in Tsaro Ta Kai Karar Mahaifinta Bisa Keta Mata Haddi Na Tsawon Shekaru a Kano Hoto: nta.ng
Asali: UGC

Likitoci sun tabbatar da zargin

Alhaji Shehu yace yayin bincike kan lamarin, an kai yarinyar asibitin Murtala Muhammad, inda masana a harkar lafiya suka tabbatar da an cutar da yaran biyu ta hanyar keta musu haddi.

Yace:

"Rahoton masana a ɓangaren lafiya ya tabbatar da cewa an cutar da matan biyu ta hanyar keta musu haddi amma karamar su, yar kimanin shekara 8, ba'a mata komai ba."
"A halin yanzun hukumar NHRC ta haɗa hannu da ma'aikatar shari'a ta kasa domin gurfanar da mahaifin, wanda aka gano jami'in tsaro ne, a gaban kotu."

Wata mahaifiya ta ɗaure ɗanta na tsawon lokaci

Hakazalika, Alhaji Shehu, yace hukumar NHRC ta fara bincike kan ɗaure wani yaro ɗan shekara 13 da mahifiyarsa ta yi a gida.

Matar, mai ƴaƴa 8, tace ita yar asalin garin Madagali ne dake jihar Adamawa, kuma ta dawo Kano ne saboda yanayin rashin tsaro a can.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dalibar Wata Jami'a, Sun Nemi a Tattaro Miliyoyi Kudin Fansa

Matar ta kara da cewa ta ɗaure yaron na ta ne saboda hana shi cutar da kansa idan ya fita daga gida domin yana da taɓin kwakwalwa.

Sai dai shugaban NHRC yace sun mika lamarin ga hukumar agajin gaggawa ta jihar Kano don ɗaukar matakin da ya dace.

A wani labarin kuma Zulum, Sarakuna, da Shugabannin Borno Sun Fadi Matakin da Zasu Dauka Kan Yan Boko Haram da Suka Mika Wuya

Shugabannin al'umma daga kowane ɓangare na jihar Borno sun gana kan mayakan Boko Haram da suka mika wuya.

Taron wanda ya kunshi shugabannin siyasa, sarakuna da na addinai ya fidda matsaya kan lamarin, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262