Wata Ƙungiyar APC Ta Bayyana Wanda Ta Ke So Ya Zama Shugaban Jam’iyyar Na Ƙasa

Wata Ƙungiyar APC Ta Bayyana Wanda Ta Ke So Ya Zama Shugaban Jam’iyyar Na Ƙasa

  • Kungiyar matasan jam'iyyar APC na dandalin sada zumunta a Arewa maso gabas ta goyi bayan Umaru Al-Makura ya zama shugaban jam'iyyar na kasa
  • Kungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunta, Mu'azu Hina, yayin zantawa da ya yi da manema labarai a garin Gombe
  • Kungiyar ta ce ta gamsu cewa Al-Makura kwararren dan siyasa ne kuma yana da ilimin da zai iya ciyyar da jam'iyyar gaba idan ya zama shugaba

Gombe, Jihar Gombe - Kungiyar Matasan Jam'iyyar All Progressives Congress, dandalin sada zumunta na Arewa maso gabas ta goyi bayan tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Al-Makura a matsayin shugaban APC na kasa, The Punch ta ruwaito.

A cewar rahoton The Punch, mai magana da yawun kungiyar, Mua'azu Hina, ne ya bayyana matsayar jam'iyyar a wani taron manema labarai a Gombe a ranar Asabar, 28 ga watan Agustan 2021.

Wata Ƙungiyar APC Ta Bayyana Wanda Ta Ke So Ya Zama Shugaban Jam’iyyar Na Ƙasa
Tsohon gwamnan Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hina ya ce:

"Bayan tattaunawa da yan jam'iyyar, kungiyoyin mata, matasa da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar All Progressives Congress a Arewa maso Gabas da wasu sassan Nigeria, Kungiyar Matasan APC na dandalin sada zumunta a Arewa maso Gabas, ta cimma matsayar cewa Umaru Al-Makura dan siyasa ne da ke kwarewa da ilimi da tabbas zai daukaka jam'iyyar APC.
"Munyi imanin cewa Al-Makura zai saurari kowa kuma zai cika alkawurran da za a yi yayin yakin neman zabe da ke tafe nan gaba a dukkan yankunan kasar."

Wani wakilin Almakura a wurin taron, Dominic Alancha, ya ce tsohon gwamnan ya yi murna da goyon bayan, musamman ganin hakan na zuwa ne daga matasan jam'iyyar wanda sune za su rike jam'iyyar a gaba.

2023: Ba mu buƙatar Atiku ya sake takara, Ya tafi Dubai ya manta da mu tunda ya sha kaye a 2019, Ƙungiyar PDP

A wani labarin daban, wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023, ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kada ya sake takara a shekarar 2023 don ya yi watsi da jam'iyyar ya koma Dubai, UAE, tunda ya fadi zabe a 2019, rahoton Daily Trust.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, bai riga ya bayyana niyarsa na son sake takara ba a 2023, amma, dansa, Adamu Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa zai sake takara.

Amma a martaninsa, Atikun ya ce ba watsi da jam'iyyar ta PDP ya yi ba, ya tafi yin karatun digiri na biyu ne a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel