Gaba da gabanta: Buhari ya dawo da Darektocin Gwamnati 11 da aka yi wa ritaya da karfi da yaji

Gaba da gabanta: Buhari ya dawo da Darektocin Gwamnati 11 da aka yi wa ritaya da karfi da yaji

  • Kwanakin baya ma’aikatar DPR ta yi wa wasu manyan ma’aikatanta ritaya
  • Wadannan ma’aikatan sun kai korafi har zuwa ofishin Muhammadu Buhari
  • An yi bincike an gano babu dalilin korarsu daga aiki, an umarci a dawo da su

Abuja - Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba hukumar DPR umarni ta dawo da wasu manyan ma’aikatanta da ta yi wa ritaya kwanaki.

Wani rahoto da Jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna cewa a watan Maris da ya wuce ne DPR ta tura wasu mataimakan darektoci 11 su tafi hutun ritaya.

Wadannan ma’aikata su 11 da suke ganin an yi masu ritaya ba tare da kwakkwaran dalili ba, sun kai kara wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Su wanene wadanda abin ya shafa?

Rahoton yace Darektocin da DPR ta sallama a wancan lokaci su ne; Dr. M.M. Zagi, Sani Hassan, A. Buba, E. Amadasu, A. R.Shakur, da kuma U.B. Nkanda.

Kara karanta wannan

Tattaunawa da Ortom: 'Yan jaridan Channels TV sun kwashe sa'o'i a hannun jami'an DSS

Ragowar sun hada da; M.A. Alaku, A.E.Antaih, Bassey Nkanga, Isa Tafida da kuma J.M.Ajewole.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka ba su takardar ajiye aiki, sai Darektocin duk suka hadu, suka rubutu wasikar korafi zuwa ga Muhammadu Buhari a matsayinsa na Ministan mai.

Daily Trust ta ce ma’aikatan sun kai kuka cewa ba su cika sharudan ritaya ba, domin ba su yi shekara 35 a aiki ba, sannan ba su shekara 60 a Duniya ba.

Buhari
Buhari ya hadu da Osinbajo Hoto: @Femi Adesina
Asali: Facebook

Rahoton binciken da HoS ta kai wa shugaban kasa

Bayan Mai girma Buhari ya samu korafinsu, sai ya umarci shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ta binciki ainihin abin da ya faru a ma’aikatar.

Da ofishin HoS ya tuntubi DPR domin jin dalilin yi wa ma’aikatan ritaya, sai aka fada mata cewa ba su yin biyayya, sannan ba su da wani amfani a ofis.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Mun taba yi wa mutum 76 jana’iza a lokaci guda, babu wanda ya ji labari inji Sultan

A karshe shugaban ma’aikatan gwamnati ta tabbatar da cewa an sallame su ne ba bisa hakki ba, ta shaida wa shugaban kasa za a iya kai gwamnati kotu.

Wannan ya sa babban hadimin shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya aika takarda zuwa ga ma’aikatar DPR, ya umarci a dawo da wadannan mutane.

Wasu suna sukar dokar PIA

A makon jiya ne aka ji cewa wasu kungiyoyin Kudu sun ce Jihohin Arewa za su fi mutanen Neja Delta cin moriyar dokar PIA da aka shigo da ita kwanaki.

Kungiyoyn Ilana Omo Oodua suna barazanar za su kai Gwamnatin Tarayya kotu domin a soke dokar PIA domin ta na kokarin azurta yankin Arewa ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel