Shugaba Buhari na kokarin jawo Arewa ta fi Kudu arziki ta dokar mai, da karfi-da yaji inji NINAS
- Kungiyoyin da ke neman a raba Najeriya sun yi tir da sabuwar dokar PIA
- Ilana Omo Oodua tana zargin cewa ana neman a sa Arewa ta fi Kudu arziki
- Banji Akintoye yace idan aka tafi a haka, sai Arewa ta fi cin moriyar dokar
Shugaban kungiyar Ilana Omo Oodua, Farfesa Banji Akintoye da wasu masu neman raba Najeriya, sun yi tir da sabuwar dokar PIA da aka sa wa hannu.
Banji Akintoye sun nuna adawarsu
Punch tace Banji Akintoye da takwarorinsa sun soki wannan dokar ta mai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan ta a kwanaki.
A wani jawabi da kungiyoyin masu fafutukar barka Najeriya suka fitar a ranar Juma’a, sun zargi manyan Arewa da kokarin karbe arzikin kudancin kasar.
Kungiyoyin sun kuma zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kokarin sa Arewa ta fi Kudu arziki.
Kungiyoyin suna karkashin lemar NINAS; Ilana Omo Oodua ta na wakiltar Kudu maso yamma, Middle Belt Renaissance tana wakiltar Arewa maso tsakiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar ta ce Lower Niger Congress tana wakiltar ‘Yan kudu maso kudu da kudu maso gabashin kasar.

Asali: UGC
'Yan Arewa aka yi wa dokar PIA
Akintoye da Sakatarensa, Tony Nnadi, sun ce Sokoto, Kebbi, Jigawa da Katsina za su amfana da PIA fiye da orinsu Akwa Ibom, Ondo, Delta, Abia, Imo da Ribas.
NINAS tace dokar ta PIA ce babbar satar karnin zamanin nan da aka yi wa mutanen Kudu, inda wasu daidaikun masu rike da madafan iko ke kokari nakasa su.
Jami’in yada labarai na kungiyar, Maxwell Adeleye ya shaida cewa za su bi matakan da doka ta tanada domin a soke wannan dokar da ke neman azurta Arewa.
Da gaske PIA za ta azurta Arewa?
NNPC tayi karin-haske ta ce ribar 3% da za a rika ware wa jihohin da aka hako mai ya zarce 30% na ribar NNPC da za kashe domin gano wasu sababbin rijiyoyi.
Binciken da The Cable ta yi, ya nuna 3% zai fito ne daga dukkanin ribar da aka samu daga mai, yayin da 30% na ribar NNPC ya kunshi fetur ne da gas kurum.
Asali: Legit.ng