Kano: 'Yan sanda sun damke mahaifiyar da ta garkame tare da hana dan ta abinci

Kano: 'Yan sanda sun damke mahaifiyar da ta garkame tare da hana dan ta abinci

  • Wata mata mai suna Maryam Dauda a Kano ta shiga hannun 'yan sandan dake Unguwar Liman Dorayi
  • Ana zargin ta da garkame yaron ta mai tabin hankali a daki tare da hana shi abinci na tsawon shekaru
  • Matar ta alakanta mugun aikin ta da matsalar talauci inda tace haka sauran yayyin shi 2 suka rasu da tabin hankalin

Kano - Wata mata a jihar Kano ta shiga hannun 'yan sanda sakamakon kama ta da laifin garkame dan ta mai shekaru 12 da tayi tare da hana shi abinci na tsawon shekaru.

Daily Trust ta wallafa cewa, Maryam Dauda ta shiga hannun 'yan sandan jihar Kano ne bayan an kama ta laifin garkame dan ta a wani daki a gidan da suke a Unguwar Liman Dorayi dake karamar hukumar Gwale ta jihar ba tare da bashi abinci ba da kuma kula da lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Garin Dadi: Kasar turai, inda za ka iya sayen katafaren gida a kasa da N500

Kano: 'Yan sanda sun damke mahaifiyar da ta garkame tare da hana dan ta abinci
Kano: 'Yan sanda sun damke mahaifiyar da ta garkame tare da hana dan ta abinci. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cewa har yanzu matar tana hannunsu kuma za a gurfanar da ita nan babu dadewa bayan an kammala bincike.

Ya kara da cewa, an ceto yaron kuma an gaggauta mika shi asibitin Murtala Muhammad domin samun taimakon likitoci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asirin Maryam ya tonu ne bayan wani Ibrahim Danladi Satatima ya shiga gidan domin dubawa saboda zai siya.

Satatima ya sanar da Daily Trust cewa ya samu yaron a cikin daki, inda aka daure shi da sarka kuma yana cin kashin shi.

A yayin da na shiga gidan tare da mai kula da shi, na ga yaron daure a wani daki kuma yana cin kashin da yayi," yace.

Ya kara da cewa, daga bisani ya nemi taimakon makwabta amma sai suka ki bashi hadin kai wurin ceton yaron.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

Don haka sai na nemi dagacin yankin amma ban same shi ba. Mun kwashe wurin sa'a daya muna jiran shi amma bai zo ba. Na kira shi a waya amma layinsa ba ya zuwa, hakan yasa na yanke kaiwa 'yan sandan Dorayi rahoto kuma sun gaggauta daukan mataki," ya kara da cewa.

Talauci ne yasa na kulle dan cikina, Maryam

A daya bangaren, wacce ake zargi ta alakanta aikinta da fatara inda tace tun bayan da ta haifa yaron da sauran 'ya'yanta, ba ta taba samun taimako ba.

Ta kara da cewa yaron na fama da cutar tabin kwakwalwa tun da aka haife shi.

Ba shi kadai bane, hatta yayyin shi biyu da na haifa ba su da lafiyar kwakwalwa har suka rasu," tace.

Babu shakka sai mun binciko wadanda suka kashe dakarunmu, Hedkwatar tsaro ta fusata

A wani labari na daban, a ranar Talata ne hedkwatar tsaro ta lashi takobin bin sawun ‘yan bindigan da suka shiga har barikin soji ta NDA suka ragargaji sojoji kuma suka yi garkuwa da wani.

Kara karanta wannan

Hotunan katafaren gidan Prince Harry da Meghan Markle da aka narka N81.9bn wurin gina shi

Daily Trust ta ruwaito cewa, an samu rahotanni akan yadda ‘yan bindiga suka afka har cikin barikin Afaka dake NDA, Kaduna inda suka kashe manyan sojoji biyu. Basu tsaya a nan ba har sai da suka yi garkuwa da wani babban sojan.

Sakamakon faruwar lamarin ne shugaban hukumar sojin kasa, Janar Lucky Irabor ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan inda yace yanzu haka an nunka tsaro a wuraren da lamarin ya faru.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel