Kotu ta tsare mutane 8 da ake zargi da yin garkuwa da matar kwamishinan Benue
- An cafke wasu mutane da suka yi awon gaba da matar kwamishina a jihar Benue, an kuma garkamesu
- An kame su da muggan makamai da sauran kayayyakin aikata laifuka bayan samun bayanan sirri
- An maka su a kotu, inda kotun ta ba da umarnin ci gaba da adana su a gidan gyaran hali zuwa lokacin da za a yi shari'a
Benue - Wata kotun majistare da ke Makurdi ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare wasu mutane takwas a gidan yarin jihar bisa zarginsu da yin garkuwa da Ann Unenge, matar kwamishinan filaye, bincike da ma’adanai na jihar Benue.
Wadanda ake zargin sune Samuel Ogbodo, Chidi Anekwe, Monday Anyigor, John Igwe, John Nwoke, Mathias Odoh, Matthew Eze da Iorhemen Yagba, The Cable ta ruwaito.
An tuhume su da laifin hada baki, fashi da makami da ta’addanci, wadanda laifuka ne da suka saba da tanadin sassan daban-daban na dokoki na musamman na jihar Benue.
Adah Odeh, alkalin kotun, ya ba da umurnin a ci gaba da tsare su a cibiyar gyaran hali ta tarraya, har zuwa lokacin da za a yankje shawara kan shari’ar.
Tun da farko, Lauyan ‘yan sanda Rachael Mchiave, ta shaida wa kotun cewa an samu karar a sashin binciken manyan laifuka na jihar (SCID) da ke Makurdi, ta hanyar wasika mai lamba CJ: 4161/BNS/JTF/OPZ/VOL. 1/440 a ranar 2 ga Agusta.
Mchiave ta ce jami’an rundunar hadin gwiwa (JTF), karkashin jagorancin Usman Dalamin, dake aiki da rahoton bayanan sirri, sun fatattaki wata tawaga da ake zargin ta sace matar kwamishinan da direbanta a ranar 29 ga watan Yuli.
Ta ce sun nemi kudin fansa Naira miliyan 51.
Mai gabatar da kara ya kuma yi zargin cewa an kwato bindiga kirar AK-47 guda daya mai lamba 5006971, magazine guda biyu dauke da harsasai 28, harsasai guda biyu, bindigar gida da layu daga hannun wadanda ake zargin.
Ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin tare da rokon kotun da ta dage sauraron karar.
An daga sauraran karar zuwa ranar 12 ga watan Oktoba don ci gaba da magana.
Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama
Fadar shugaban kasa ta zargi gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, da kunna wutar kiyayya tsakanin mazauna a jiharsa ta hanyar kai hari kan wata kabila wanda ya zama daidai da kisan kare dangin da ya taba faruwa a Rwanda.
Babban mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin yau Laraba, 25 ga watan Agusta ta shafinsa na Facebook.
Shehu ya ce kamar yadda ya faru a Rwanda inda shugabannin Hutu na wancan lokacin suka tunzura ‘yan kasarsu a kan junansu, inda suka ce akwai "boyayyar manufar Tutsi” kan Hutu, Ortom ma haka ya ce akwai "boyayyar manufar Fulani” kan sauran kabilun jiharsa da kasar.
Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce harin baya-bayan nan da aka kai Cibiyar Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA) a Kaduna zai taimaka wajen kara azama, kaimi da sa karfin soji wajen kawo karshen tashin hankali a kasar.
Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa:
"Wannan mummunan aikin zai hanzarta kawar da munanan abubuwan da ke faruwa, wanda membobin rundunar sojin suka kuduri aniyar aiwatarwa cikin kankanin lokaci.
Asali: Legit.ng