A bari yan kabilar Igbo su balle kawai mu huta, Tsohon Jakadan Najeriya

A bari yan kabilar Igbo su balle kawai mu huta, Tsohon Jakadan Najeriya

  • Ambasada Yerima Abdullai yace gwanda a bari Igbo su kafa tasu kasar maimakon tada tarzoma
  • Tsohon Jakadan Najeriyan zuwa Malaysiya kuma dattijo yace Najeriya ba zata juri wani yakin basasa ba
  • Ya gargadi masu rajin kudu maso gabas suyi nazari kan illar abinda suke nema

Gombe - Wani tsohon jakadan Najeriya zuwa Malysiya, Ambasada Yerima Abdullah, ya yi kira ga masu rajin ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biyafara suyi nazari kan illar ballewar Najeriya.

Abdullahi, wanda makusancin Buhari ne, ya ce zai fi kyautata masu rajin su nemi zaben raba gardama saboda hakan zai fi kyau don zaman lafiya da cigaban kasar.

A bari yan kabilar Igbo su balle kawai mu huta, Tsohon Jakadan Najeriya
A bari yan kabilar Igbo su balle kawai mu huta, Tsohon Jakadan Najeriya Hoto: Ohanaeze
Asali: Facebook

Gwanda Ballewa daga Najeriya da yakin basasa

Ya bayyanawa jaridar Punch a hirar da tayi da shi ranar Talata, 10 ga Agusta cewa:

"Wannan abu ne da muka yi yakin basasa kansa kuma mutane da yawa cikinmu suka mutu, wasu kuma sun rayu. Wasu daga cikin shugabanninmu na da hankali, yawanci sun bayyana cewa ba mu bukatar wani yaki, kuma na yarda da hakan."

Kara karanta wannan

Na kusa da Buhari suna kangeshi da masu fada masa gaskiya, Dalung

"Amma idan akwai mutanen da ke ganin suna son nasu kasar. Biyafara ko wata kasa, abunda yafi dacewa shinemu basu daman zabe. A yi zaben raba gardama, idan suna son tafiya a barsu su tafi."

Abdullahi ya bayyana illar da ballewa za ta yiwa yan kasuwan Igbo saboda suna baje a dukkan sassan kasar.

Yace:

"Ya kamata su sani cewa akwai Inyamurai masu arziki a Gaboro a Borno, da kuma Ilela a Kawoje, jihar Kebbi."
"Akwai Igbo a fadin kasar nan kuma masu arziki ne. Saboda haka kawai a basu dama su tafi mu huta."

'Yan sanda sun damke babban limamin IPOB da layu tare da harsasai

Rundunar 'yan sanda ta sanar da damke babban limamin masu rajin kafa kasar Biafra, IPOB a jihar Imo, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, CSP Mike Abattam ya sanar, wanda ake zargi mai suna Ikechukeu Umaefulem, an kama shi ne a wani wurin bautar gargajiya dake karamar hukumar Ikeduru ta jihar Imo.

Kara karanta wannan

Matasan mayakan Boko Haram 14, mata da yara 31 sun sake mika wuya a Konduga

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel