Ka Ji Kunya: Sadaukin Shinkafi ya soki Mataimakin Gwamnan Zamfara kan ƙin sauya sheƙa zuwa APC
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya caccaki mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Gusau
- Hakan ya biyo bayan kin canja shekar da yayi daga jam’iyyar PDP zuwa APC bayan gwamnansa, Bello Matawalle, ya canza
- Tsohon ministan ya yi wannan caccakar ne ta wata wallafa da yayi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta ranar Talata
FCT, Abuja - Tsohon ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode (Sadaukin Shinkafi) ya yi wa Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Gusau, wankin babban bargo a kan kin komawa jam’iyyar APC.
A wata wallafa da Tsohon ministan yayi ta shafinsa na Twitter, wanda shi din jigo ne na jam’iyyar PDP, ya ce Mahdi bai nuna da’a ba ga gwamnansa, Bello Matawalle, wanda ya canja sheka daga PDP zuwa APC, premium times ta ruwaito.
Gwamnan jihar Zamfara tare da ‘yan majalisar jihar da sauran kwamishinonin jihar sun koma jam’iyyar APC a watan Yuli, bayan watanni kadan da gwamna Ben Ayade na jihar Cross River da David Umahi na jihar Ebonyi suka koma jam’iyya mai mulkin.
Idan gwamna ya koma wata jam’iyya, mai zai hana mataimakinsa koma wa? Gwamna Bello Matawalle bai zabi kowa ya kasance mataimakinsa ba sai kai, amma mai zai sa ka yi masa rashin da’a kuma ka ci amanarsa?
Ka dai ji kunya!
Premium Times ta ruwaito cewa, tsohon ministan yana matukar caccakar APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari sosai kuma ya dade yana musanta batun zai sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Rikicin jam'iyyar PDP yana cigaba da kamari
Bayan kotu ta dakatar da Uche Secondus daga zama shugaban jam’iyyar PDP, tsohon ministan ya kwatanta kokwantonsa a kan yadda za a yi jam’iyyar ta gyara matsalolin ta kafin zaben 2023.
Ko da an dage dakatarwar da aka yi cikin kwanaki kadan, da kyar matsalolin jam’iyyar su kare.
Wannan ra'ayin ka ne: FG ta yi wa Masari martani kan cewa mutane su kare kansu daga ƴan bindiga
A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta yi watsi da kiran da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina da takwararsa na Jihar Benue, Samuel Ortom, da wasu kungiyoyi da mutane suka yi na cewa mutane su kare kansu daga 'yan bindiga, rahoton Daily Trust.
Ministan Harkokin 'Yan sanda, Mohammed Dingyadi, yayin jawabin shekara-shekara na ma'aikatarsa karo na biyu a hedkwatar yan sanda a Abuja ya ce gwamnati bata goyon bayan mutane su dauki makamai da kansu.
Sannan, Ministan ya kara da cewa Masari yana da ikon fadin ra'ayinsa kamar yadda rahoton Daily Trust ya bayyana.
Asali: Legit.ng