Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga sun sace mutum 7 a sabon harin da suka kai cikin dare a Zaria

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga sun sace mutum 7 a sabon harin da suka kai cikin dare a Zaria

  • Yan bindiga sun afka unguwar Zango da ke Samarun Zaria a jihar Kaduna sun sace a kalla mutane bakwai
  • Wani shaidan gani da ido ya ce maharan sun afka unguwar ne da tsakar dare a lokacin mutane suna barci
  • Ya ce sun rika shiga gidaje da tsakar daren sannan sun shafe kimamin mintuna 30 suna ta harbe-harbe kafin suka tafi

Zaria, Jihar Kaduna - A kalla mutane bakwai ne wasu yan bindiga suka sace yayin da suka kai hari a unguwar Zango a Samarun Zaria da ke jihar Kaduna, The Cable ta ruwaito.

Rahotanni sun ce 'yan bindigan sun afkawa unguwar ne ta hanyoyin shiga daban-daban misalin karfe dayan daren Juma'a a yayin da mutane ke barci.

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun sace mutum 7 a sabon harin da suka kai cikin dare a Zaria
Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun sace mutum 7 a sabon harin da suka kai cikin dare a Zaria
Asali: Original

Kara karanta wannan

Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace

Wani shaida ya ce:

"Yan bindigan sun kai hari wasu gidaje a yankin a yayin da suke ta harbe-harben bindiga na tsawon mintuna 30.
"Dan uwa na ya fara kira na a waya, yana cewa masu garkuwa da mutane sun shigo Zango, daga nan na fara jin karar harbin bindiga a gaban gidanmu. Nan take na tafi na duba 'ya'ya na na gano suna barci."
"Na leka ta tagar; domin ina tunanin sun riga sun shigo gidan mu ne. Sun buga kofar gidan mu sau uku sannan suka sha ruwa a famfon da ke kofar gidan a waje.
"Duk wanda ka kira sai ya ce maka sun wuce ta kofar gidansu. Kawo yanzu an fada masa mutum bakwai aka sace. Abin da muka sani kenan yanzu. Sun shiga gidaje da yawa. Ina da tabbacin sun sace fiye da hakan."
Kakakin yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige bai daga wayarsa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana ba a lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya sakamakon kashe tsohon ɗan kwallon Nigeria da aka yi a rikicin Jos

A baya-bayan nan dai yan bindiga suna yawan kai hare-hare a sassan jihar Kaduna.

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Sace Sakataren NASIEC a Nasarawa

A wani labarin daban, Ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace Mohammed Okpu, sakataren Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Jihar Nasarawa, The Cable ta ruwaito.

Hakan na cikin wata sanarwar ne da mai magana da yawun yan sandan jihar Nasarawa, Rahman Nansel, ya fitar a ranar Laraba a Lafia.

The Cable ta ruwaito cewa Nansel ya ce kimanin yan bindiga biyar ne suka kutsa gidan sakataren na NASIEC a ƙauyen Bakin Rijiya da ke hanyar Lafia-Shendam misalin ƙarfe 11.45 na daren Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164