Nadin mukami: Shugaban kasa ya amince da nadin Dr. Simon Harry a matsayin Shugaban NBS

Nadin mukami: Shugaban kasa ya amince da nadin Dr. Simon Harry a matsayin Shugaban NBS

  • Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabon shugaba a hukumar NBS
  • Zaman Yemi Kale ya kare bayan wa’adinsa sun kare a watan Agustan nan
  • Darektan tsare-tsare, Dr. Simon Harry ne zai dare kujerar shugaban na NBS

Abuja - Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabon shugaban hukumar NBS mai alhakin tattara alkaluma a Najeriya.

Harry ya canji Yale - Minista

Jaridar Punch ta ce Dr. Simon Harry ne sabon shugaban NBS na kasa. An fahimci wannan ne a wani jawabin da Ministar tattali da kasafin kudi ta fitar.

Wani hadimin Ministar wajen hulda da jama’a, Yunusa Abdullahi ya bada sanarwar nada Dr. Simon Harry a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta, 2021.

Yunusa Abdullahi ya yi wa jawabin take da ‘Shugaba Buhari ya amince da Dr. Simon Harry a matsayin sabon shugaban mai tattara alkaluma na kasa.”

Kara karanta wannan

Kalaman Gwamnan Arewa kan zaben 2023 ya tsokano masa fada da Magoya-bayan Tinubu

Harry zai maye gurbin Yemi Kale wanda wa’adinsa na biyu ya cika a ranar 16 ga watan Agusta, 2021.

Wanene Simon Harry?

Kafin yanzu, Dr. Harry shi ne darektan tsare-tsare na hukumar NBS. Bugu da kari ya yi shekaru kusan 30 a kan wannan aiki na tattara alkaluma a Najeriya.

Dr. Simon Harry
Shugaban National Bureau of Statistics Hoto; premiumtimesng.com
Asali: UGC

Premium Times ta ce sabon shugaban na NBS ya soma aiki a gwamnatin tarayya ne tun a 1992. A shekarar 2019 ya samu kai wa mataki na Darekta a ofis.

Jawabin Ministar ya bayyana cewa Simon Harry na cikin wadanda suka taka rawar gani a gyare-gyaren da aka kawo wajen maida NBS yadda ta ke a yau.

Rahoton yake cewa a baya an san hukumar ta NBS ne da ofishin alkaluma na gwamnatin tarayya.

Hukumar dillaci labarai na kasa, NAN tace da Harry ne ya yi sanadiyyar da hukumar tarayyar ta kafa rassa a matakan jihohin kasa da yankunan Najeriya.

Kara karanta wannan

Kungiyar kare hakkin jama'a ta kai karar Buhari a kotu kan ‘bacewar’ Naira Biliyan 106 a 2018

Gwamnati ta dawo da GEEP 2.0 a 2021

A makon nan ne Sadiya Umar Farouk ta bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta dawo da GEEP 2.0, domin ceto mutane miliyan 100 daga talauci.

Za a yaye talaucin a cikin mata marasa karfi, da matasa marasa abin yi da marasa galihu ne ta tsare-tsaren TraderMoni, FarmarMoni da kuma MarketMoni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel