Kalaman Gwamnan Arewa kan zaben 2023 ya tsokano masa fada da Magoya-bayan Tinubu
- Tinubu Support Group ta yi wa Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello raddi
- Kungiyar TSG ta maida martani ne bayan Gwamnan ya tabo Bola Tinubu
- Bello ya ba Tinubu shawara ya hakura da 2023, ya bar yara da shugabanci
Wasu daga cikin magoya bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a karkashin tafiyar Tinubu Support Group sun maida wa gwamnan Kogi martani.
Jaridar Punch ta kawo rahoto a ranar 23 ga watan Agusta, 2021, cewa kungiyar Tinubu Support Group ta fusata da kalaman da gwamnan ya yi.
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya takalo magoya bayan jigon na APC ne bayan ya yi kira a gare shi ya hakura da n shugaban kasa a 2023.
Tinubu Support Group ta caccaki Yahaya Bello ta ce ya ci amanar tafiyar the Not-too-Young-to-Run domin babu abin da ya tabuka a jihar Kogi.
Rahoton yace kungiyar ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar ta bakin shugabanta, Umar Ibrahim.
Da yake jawabi a birnin tarayya Abuja, Alhaji Umar Ibrahim yace duk mutanen Najeriya sun sallama cewa gwamna Bello ya ba matasa kunya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Raddin da TSG ta yi wa Gwamna Bello
“Ta ya za mu damka kasa irin Najeriya ga mai ikirarin shi matashin gwamna ne wanda ya damalmala komai da aka ba shi mulkin jiharsa?”
“Bello ne gwamnan da ya fi kowane shafe watanni bai biya albashi ba, ya gagara tabuko komai duk da kudin da yake samu a gida da waje.”
“Muna kira gare ka da ka maida hankali wajen kiran mutanen da ka wahalar a jihar Kogi su yafe maka, a maimakon harin kujerar shugaban kasa.”
Kungiyar ta Tinubu Support Group ta ce Bola Tinubu ne wanda ya fi dace wa ya rike Najeriya a 2023, a lokacin da Muhammadu Buhari zai sauka.
Abin da ya jawo surutu
Da aka yi hira da shi, Yahaya Bello ya ce akwai bukatar Bola Tinubu ya bar matasa su karbi ragamar mulki, yace babu ruwansa da wata yarjejeniya.
Gwamnan yake cewa Almajirai masu bara da masu saida tumatur suna rokonsa ya yi takarar shugaban kasa, kuma ya yi alkawari ba zai ba su kunya ba.
Asali: Legit.ng