Mutum miliyan 1 za su amfana, Gwamnati ta maido TraderMoni, MarketMoni, FarmerMoni

Mutum miliyan 1 za su amfana, Gwamnati ta maido TraderMoni, MarketMoni, FarmerMoni

  • Gwamnatin Muhammadu Buhari ta shigo da sabon samfurin tsari na GEEP 2.0
  • Marasa karfi za su amfana da TraderMoni, MarketMoni, da kuma FarmerMoni
  • An kuma kara kudin da ake rabawa matasa, manoma da kananan ‘yan kasuwa

Abuja - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin nan na Government Enterprise and Empowerment Programme wanda aka fi sani da GEEP.

The Cable tace wannan karo an yi wa shirin sabon tsari, aka sa masa suna GEEP 2.0 da nufin a ceto mutane miliyan 100 daga kangin talauci a Najeriya.

Ministar bada agajin gaggawa da walwalar jama'a, Sadiya Umar Farouq ta kaddamar da wannan shiri ranar Talata, 25 ga watan Agusta, 2021 a garin Abuja.

Sadiya Umar Farouq take cewa wannan shiri ya na cikin tsare-tsaren NSIP da gwamnatin tarayya ta shigo da shi domin tallafa wa marasa karfi da galihu.

Kara karanta wannan

PIA: Gwamnati ta janye damar musamman da aka ba BUA, Dangote su shigo da mai daga waje

Ministar tace wannan karo shirin GEEP zai tallafi wadanda ba su ci moriyar sauran tsare-tsaren da aka kawo domin taimaka wa ‘yan kasuwa da jari ba.

Abin da Ministar ta fada

"GEEP ya zo ne a samfurori uku – TraderMoni da aka kawo domin matasan da ba ayi da su, MarketMoni – na mata marasa karfi, sai FarmerMoni – wanda zai maida hankali a kan manoman da ke karkara."

Sadiya Umar Farouq
Hajiya Sadiya Umar Farouq Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

‘Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a yalwata tsarin, a bada bashin kudi ga karin mutane miliyan daya da za su ci moriyar shirin.”
“Za a maida hankali a kan kananan manoma a shekarar 2020/2021, an canza wa GEEP fasali, an kaddamar da tsarin GEEP samufuri na 2.0 a yau.”
"GEEP 2.0 zai taimaka wa mata, matasa marasa aikin yi, da sauran marasa galihu a cikin al’umma."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

“Ina so in bayyana cewa an tsara GEEP 2.0 da kyau wannan karo ta yadda aka samu wakilai daga tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomin Najeriya.”

Najeriya za ta kera jirage

Gwamnatin tarayya za ta hada-kai da wani kamfanin waje, Magnus aircraft manufacturing industry, za a rika kera jiragen sama kafin karshen shekarar 2023.

Ministan harkokin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika ya kai ziyara zuwa kasar Hungary, ya nuna ya na so Najeriya ta koma kera jiragen sojojin yaki marasa nauyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng