Matsalar Tsaro: Babu Sauran Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan Arewa
- Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, yace babu sauran yan bindiga a faɗin jihar Neja
- Gwamnan yace a halin yanzun sai dai yan bindiga su zo daga makotan jihohi su aikata ta'addanci su koma
- Gwamnan ya kuma jinjina wa jami'an tsaro bisa jajircewarsu tare da alkawarin samar musu da abinda suke bukata
Niger - Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, yace haɗin guiwa tsakanin jihohin da ayyukan yan bindiga ya shafa zai kawo karshen aikata manyan laifukansu na satar mutane.
Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yakai ziyara kauyen Ma'undu, karamar hukumar Mariga, a jihar Neja.
Legit.ng hausa ta gano cewa gaba ɗaya mutanen kauyen sun tsere saboda yawaiyar hare-haren yan bindiga a yankin.
Gwamna Bello ya kai wannan ziyara ne da nufin kara karfafa wa jami'ai 300 da suka haɗa da yan bijilanti a kokarinsu na ceto garin, sanna ya ga irin ɓarnar da aka yiwa mutanen garin.
Wannna na kunshe ne a wani rubutu da sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Mary Noel-Berje, ya buga a Facebook.
Babu sauran sansanin yan bindiga a Neja
Bello ya bayyana cewa babu sauran yan bindiga a faɗin jihar, inda ya kara cewa suna zuwa ne daga makotan jihohi domin aikata ta'addancinsu.
Gwamna Bello yace:
"Babu sauran sansanin yan bindiga a jihar Neja, yanzun sai dai suzo daga makotan jihohi musamman Zamfara, su aikata ta'addanci su koma. Amma a yanzun babu sauran su a jihar mu."
Zamu cigaba da kokarin tsare al'umma
Bello ya kara da cewa gwamnatinsa zata cigaba da kokarin da take na tsare rayukan al'umma musamman yankunan da lamarin rashin tsaro ya shafa kamar Ma'undu.
Ya kuma jinjina wa jami'an tsaro bisa namijin kokarin da suka yi wajen fatattakar yan bindiga suka bar kauyen tare da alkawarin tallafa musu da kayan aiki da kuma walwala.
A wani labarin kuma Liyafa Ta Cigaba, Tsohon Shugbaan Kasa Jonathan Ya Samu Babban Mukami a Kasar Waje
An rantsar da tsohon shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Jonathan, a matsayin sabon shugaban jami'ar Cavendish, Uganda.
Tsohon shugaban ya zama mutum na uku da zai jagoranci jami'ar tun bayan da aka kafa ta.
Asali: Legit.ng