Da Dumi-Dumi: Matawalle Ya Yi Kira Ga Gwamnatin Buhari Ta Saka Dokar Ta Baci a Arewacin Najeriya

Da Dumi-Dumi: Matawalle Ya Yi Kira Ga Gwamnatin Buhari Ta Saka Dokar Ta Baci a Arewacin Najeriya

  • Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira da a saka dokar ta bace a arewacin Najeriya baki ɗaya
  • Gwamnan yace yana da yakinin idan aka ɗauki wannan matakin za'a shawo ƙan matsalar tsaron da ta addabi yankin
  • Arewacin Najeriya na fama matsalolin Boko Haram, ISWAP da kuma ayyukan yan bindiga

Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira a saka dokar ta baci a yankin arewacin kasar nan kan kalubalen tsaron da yaki ci yaki cinyewa, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Gwamanan ya yi wannan kiran ne a gidan gwamnatin jihar dake Gusau, yayin gana wa da mataimakin sufeto janar na yan sandan kasar nan, Ali Janga, ranar Laraba.

Gwamnan ya nuna matukar damuwarsa kan jerin hare-haren da ake cigaba da kaiwa mafiyawancin jihohin yankin arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Matasan Jos sun kwace gawawwakin mutanen da aka kashe daga asibiti, sun kai ofishin gwamna da majalisa

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle
Da Dumi-Dumi: Matawalle Ya Yi Kira a Saka Dokar Ta Baci a Arewa Maso Yamma Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Bugu da kari matawalle yace yana da yakinin saka dokar ta ɓaci zai kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi arewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Arewacin Najeriya ya kunshi yankunan arewa maso gabas, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya kuma ya kunshi jihohi 19 da babban birnin tarayya Abuja.

Menene babbar matsalar yankin?

Shekaru da dama da suka shuɗe, wasu sassa na arewa na fama da aikata manyan laifuka da suka haɗa da satar mutane, tada bama-bamai, da kuma kai hari kauyuka da garuruwa.

Zuwa yanzun, ɗaruruwan dubbanin mutane sun rasa rayukansu a yankin yayin da wasu miliyoyi aka tilasta musu barin mahallansu.

Boko Haram da ISWAP sune manyan kungiyoyin dake da alhakin hare-haren dake faruwa a yankin arewa maso gabas, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito

Yayin da yan bindiga dake satar mutane domin neman kuɗin fansa suka addabi arewa maso yamma da kuma wani sashi na arewa ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An kashe mutane masu yawa, an yi ƙone-ƙone yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos

Shugaban PDP ya kwanta dama

A wani labarin kuma Shugaban Jam'iyyar PDP, Adegbola Dominic, Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Shugaban babbar jam'iyyar adawa PDP, reshen jihar Lagos, Adegbola Dominic, ya kwanta dama..

Kakakin jam'iyyar na jihar, Taofeeq Gani, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Yace za'a sakko da tutocin PDP dake faɗin jihar Lagos zuwa rabi domin nuna alhinin mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262