Liyafa Ta Cigaba, Tsohon Shugbaan Kasa Jonathan Ya Samu Babban Mukami a Kasar Waje

Liyafa Ta Cigaba, Tsohon Shugbaan Kasa Jonathan Ya Samu Babban Mukami a Kasar Waje

  • Tsohom shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya zama shugaban jami'ar Cavendish ta kasar Uganda
  • Tsohon shugaban ya zama mutum na uku da zai jagoranci jami'ar tun bayan da aka kafa ta
  • Rahotanni sun bayyana cewa Jonathan ya fara aiki nan take, inda ya jagoranci bikin yaye dalibai karo na 10

Abuja - An rantsar da tsohon shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Jonathan, a matsayin sabon shugaban jami'ar Cavendish, Uganda.

Tsohon shugaban ya sanar da wannan cigaba da ya samu a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook, inda ya haɗa da wasu zafafan hotuna yayin rantsar da shi a sabon mukamin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Jonathan shine shugaban jami'ar Cavendish na uku tun bayan kafa makarantar.

Goodluck Jonathan a wurin taron yaye dalibai
Liyafa Ta Cigaba, Tsohon Shugbaan Kasa Jonathan Ya Samu Babban Mukami a Kasar Waje Hoto: Goodluck Jonathan FB fage
Asali: Facebook

A rubutun da Jonathan ya yi a facebook, yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

2023: APC na fuskantar sabuwar barazana yayin da Atiku da Obaseki suka hadu kan yadda PDP za ta kada jam'iyyar

"Ina farin cikim sanar da ku cewa an rantsar da ni a hukumance a matsayin shugaban jami'ar Cavendish, kuma har na fara gudanar da aiki na a wurin bikin yaye ɗalibai karo na 10 yau a Kamfala, Uganda."
"Ina taya ɗaliban da aka yaye murna tare da rokon su da su yi amfani da ilimin su wajen tallafawa mutane, gina al'umma ta gari da kuma samar da cigaba a yankunansu."

Shugabannin jami'ar da suka gabaci Jonathan

Tdohon shugaban ƙasar Zambia, marigayi Kenneth Kaunda, shine ya fara jagorantar jami'ar a karon farko bayan kafa ta.

Yayin da tsohon shugaban haɗaɗɗiyar jamhuriyar Tanzania, marigayi Benjamin Mkapa, ya zama shugaba na biyu da ya jagoranci jami'ar.

A wani labarin kuma NBC Ta Tuhumi Channels TV Kan zafafan kalaman Gwamna Ortom

Hukumar kula da kafafen watsa labarai ta ƙasa (NBC), ta tuhumi Channels tv kan maganganun da Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, ya yi a shirinta na Sunrise daily ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Tsige Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa Secondus

NBC ta aike da takarda ga kafar tare da bata wa'adin kwana ɗaya tayi bayani dalla-dalla kan watsa kalaman gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel