Afghanistan: Wata kungiya ta bullo domin kalubalantar mulkin Taliban, ta harba makami

Afghanistan: Wata kungiya ta bullo domin kalubalantar mulkin Taliban, ta harba makami

  • A can kasar Afghanistan, an samu wasu sojojin da suke adawa da mulkin kungiyar Taliban
  • Rahoto ya bayyana cewa, sun harba wani babban makami cikin kwari domin nuna adawarsu ga Taliban
  • Sun kuma bayyana manufarsu na kifar da gwamnatin kungiyar Taliban matukar ta yi yunkurin kai musu farmaki

Afghanistan - A saman wani tsauni mai mamayewar bakin haure tsawon shekaru da dama, wasu mayakan dake adawa da mulkin Taliban sun harba babban makami a cikin wani kwari mai zurfi a Panjshir, AlJazeera ta ruwaito.

Mayakan sun kasance mambobi ne na National Resistance Front (NRF) - babbar fitacciyar kungiyar adawa ta Afganistan da ta fito tun lokacin da Taliban ta kame Kabul kwanaki tara da suka gabata.

Afghanistan: Wata sabuwar kungiya ta bullo domin kalubalantar mulkin Taliban
Sojojin Panjshir | Hoto: aljazeera.com
Asali: UGC

Tare da mayakan kungiyar da tsoffin sojojin gwamnati masu mukamai, NRF ta kafa buhunan bindigogi, harsasai da wuraren sa ido wadanda aka yi da buhunna cike da kasa don kare farmakin Taliban a sansaninsu da ke a Kwarin Panjshir.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka sace ɗalibin NDA kuma ɗan alƙali a Kaduna

Mayakan, da yawa suke sanye da kakin sojoji, suna sintiri a yankin a cikin manyan motocin Humvees masu dauke da bindigogi a baya da aka ce kirar Amurka ne.

Wani mayaki a tsaunin na Panjshir, da yake lissafa nasarorin da suka samu a baya kan 'yan Taliban ya ce:

"Za mu goga fuskokinsu a cikin kasa."

Su waye a asalin yankin Panjshir?

A tsaunin dake da cikakken tsaro, an ce mafiya yawan mutanen wajen 'yan kabilar Tajik ne, wasu mazauna yankin a Afghanistan.

Ahmad Massoud, daya daga cikin shugabannin NRF, ya shaida wa Washington Post a makon da ya gabata cewa:

"Idan mayakan kungiyar Taliban suka kaddamar da hari, ba shakka, za su fuskanci tasku daga gare mu."

Ahmad Massoud, shi ne dan shugaban Tajikistan Ahmad Shah Massoud, wanda ake jinjinawa bisa canza kwarin Panjshir zuwa wani yanki na adawa da mayakan Rasha da Taliban.

Kara karanta wannan

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

Lardin Panjshir yana karkashin ikon NRF wanda The Khaama Press ta ruwaito cewa, akalla tsoffin membobin gwamnatin biyu suna can, ciki har da ministan tsaro da mataimakin shugaban kasa na farko.

Dakarun Amurka sun gana da shugabannin Taliban kan batun Amurkawa

A wani labarin, Amurka ta bayyana cewa dakarunta sun gana da shugabannin Taliban da suka kwace mulki a kasar Afghanistan, in ji Aminiya.

Kakakin Sakataren Tsaron Amurka, John Kirby, ya ce kwamandojin kasar da ke filin jirgin sama na Kabul, babban birnin Afghanistan na ganawa da Taliban “a matakin Afghanistan, muna kuma tattaunawa da su kan kwaso Amurkawa”.

The Columbian ta ruwaito cewa, Kirby shaida wa ’yan jarida a Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) cewa:

“Nan gaba ne za a san me zai faru, amma tabbas kwamandojinmu suna magana da shugabannin Taliban domin kammala aikin da suka je yi a can."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.