Kungiya na bukatar a fattaki NSA, tace harin NDA na nuna lalacewar tsaro

Kungiya na bukatar a fattaki NSA, tace harin NDA na nuna lalacewar tsaro

  • A ranar Talata Kungiyar dattawan arewa ta bayyana harin da ‘yan bindiga suka kai barikin Afaka dake NDA a matsayin raunin tsaro a kasar nan
  • Shugaban kungiyar CNEPD ta bayyana takaicin ta a wata takarda wacce shugabanta, Zana Goni ya saki, inda yace babu wanda ya tsira kenan a Najeriya
  • Don haka ne ya bukaci a yi gaggawar tsige NSA, Manjo janar Babagana Monguno daga kujerarsa inda yace a cire shi matsawar ya ki murabus

Kaduna - A safiyar Talata ne kungiyar dattawan arewa ta koka a kan tabarbarewar rashin tsaro sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai barikin Afaka dake NDA.

Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban kungiyar CNEPD, Zana Goni ya bayyana hakan ne a wata takarda da ya saki inda yace duk matsayin mutum da kuma inda yake zama ba zai tsira daga ta’addanci ba kenan a kasar nan.

Kara karanta wannan

Da wanne ido zaku kallemu, kun ji kunya sosai, 'Yan Najeriya sun caccaki hukumomin NDA

Kungiya na bukatar a fattaki NSA, tace harin NDA na nuna lalacewar tsaro
Kungiya na bukatar a fattaki NSA, tace harin NDA na nuna lalacewar tsaro. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kungiya ta bukaci a tsige Monguno

Sakamakon haka ne ya bukaci a tube mai bayar da shawara a kan harkar tsaro na kasa, Manjo janar Babagana Monguno mai murabus, matsawar yaki sauka da kansa.

Bayan kashe sojojin da suka yi harin wasu sun jigata wadanda yanzu haka suna asibitin NDA ana kulawa da lafiyarsu, Daily Trust ta ruwaito.

Dattawan sun ce ya kamata a kawo garanbawul a kan harkar tsaron Najeriya gaba daya, kuma ya kamata manyan shugabannin tsaron kasar nan su fuskanci tuhuma.

Ya nuna alhininsa a kan yadda shugaba Muhammadu Buhari ya kyale Monguno ya cigaba da aiki duk da ya canja shugabannin tsaro

2023: Hadimin Osinbajo ya bayyana ra'ayin ubangidansa kan tsayawa takarar shugabancin kasa

A wani labari na daban, Laolu Akande, mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya ce ubangidansa bai bayyana burinsa na takarar shugabancin kasa ba, akasin yadda ake ta yadawa a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

A wata takarda da Akande ya fitar a ranar Litinin, ya ce mataimakin shugaban kasan ya mayar da hankali ne wurin aiki kan matsalolin da kasar nan ke fama da su.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya kwatanta rahotannin da hanyoyin dauke masa hankali inda ya shawarci masu wannan wallafar da su daina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel