Rashin tsaro: 'Yan Najeriya ba su cancanci wannan ba - Majalisar wakilai
- Mambobin kungiyar marasa rinjaye a majalisar wakilai sun koka kan halin da kasar ke ciki na rashin tsaro
- Sun kuma bayyana cewa 'yan Najeriya basu cancanci shiga wannan mawuyacin yanayi da suke ciki ba
- A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar, sun nemi a yi bincike kan harin da 'yan bindiga suka kai NDA
Abuja - Mambobin kungiyar marasa rinjaye a majalisar wakilai sun bayyana cewa 'yan Najeriya ba su cancanci halin da suke ciki ba wanda ya zama ruwan dare a baya-bayan nan.
Koken nasu wanda ke kunshe a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai, Ndudi Elumelu, yana magana ne a kan karuwar ayyukan ta’addanci da hare -haren ‘yan bindiga a cikin kasar.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“'Yan Najeriya ba su cancanci shiga cikin wannan mummunan yanayin ba.”
‘Yan majalisar sun kuma bukaci jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke jagorantar gwamnatin da ta dauki tsauraran matakai don ceto ‘yan Najeriya daga rashin tsaro, Channels TV ta ruwaito.
Mambobin hamayyar a zauren majalisar sun ci gaba da cewa sun firgita, musamman kan mamayar da aka kaiwa Kwalejin horar da sojojin Najeriya (NDA) wanda ya haifar da kisa da sace wasu jami’an soji.
Sun koka kan yadda ake kai hare-hare sansanonin soji da kuma kisan ganganci da ‘yan bindiga ke yiwa ‘yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba duk da tabbacin da ake samu daga gwamnati mai ci.
Bayan dogon nazari, 'yan majalisar sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa don magance mummunan halin da ake ciki da kuma ceto kasar daga durkushewa.
Sun kuma nemi a gaggauta gudanar da bincike kan yanayin da ya ba da damar mamaye NDA da kashe -kashe da sace jami'an, Vanguard ta ruwaito.
A wani labari na daban, wadanda suka yi garkuwa da yaran makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko sun bayyana cewa biyar daga cikin yaran da ke tsare suna cikin mawuyacin hali kuma suna iya mutuwa nan ba da jimawa ba.
Shugaban makarantar, Alhassan Garba Abubakar, ya ce masu garkuwar sun fada masa haka a hirar su ta karshe.
Masu garkuwa da mutanen, sun ce a shirye suke su karbi kudin fansa na farko na naira miliyan 18 domin sakin yaran ga iyayensu.
Asali: Legit.ng