Wasu ‘Yan bindiga sun sace Mai takaba kwana 1 da mutuwar Maigidanta a jihar Katsina

Wasu ‘Yan bindiga sun sace Mai takaba kwana 1 da mutuwar Maigidanta a jihar Katsina

  • ‘Yan bindiga sun je gidan makoki, sun dauke mutae biyar a kauyen Katsina
  • Miyagun sun auka gidan Marigayi Dagacin Kofa da ya rasu cikin makon nan
  • Har yanzu Bazawarar da Marigayi Dagacin ya bari tayi masa takaba na tsare

Katsina – Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da bazawarar da Dagacin kauyen Kofa, karamar hukumar Kusada a jihar Katsina, Alhaji Rabe Bello Kofa.

'Yan bindiga sun fada gidan makoki

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ‘yan bindiga sun shiga kauyen cikin tsakar daren Laraba, 25 ga watan Agusta, 2021, suka sace wannan baiwar Allah.

Majiyar ta shaida wa jaridar cewa wadannan miyagu suna shigo wa garin, ba su zarce a ko ina ba sai gidan marigayin, dagacin da ya rasu a ranar Talatar nan.

Kara karanta wannan

Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara

A nan ne ‘yan bindigan suka yi gaba da matar da marigayin ya bari, da wasu a cikin ‘yanuwansa.

Jaridar Manuniya ta kawo wannan labari inda ta ce ‘yan bindigan sun shigo cikin dare, suka kora wadanda suka samu suna zaman makoki, suka shiga jeji.

Wani mazaunin kauyen ya shaida wa manema labarai cewa an fito da sauran wadanda aka dauke, wanda ta rage ita ce wanda ta ke yi zaman takaban.

Gwamnan jihar Katsina a Aso Villa
Buhari da Aminu Bello Masari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya abin ya auku?

“Dagacin Kofa wanda yaya ne a wurin wani tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Katsina ya rasu a ranar Talata, kuma an yi masa jana’iza tun a ranar.”
“Abin takaici, wasu ‘yan bindiga sun shiga gidan, sun dauke mutane biyar daga cikin ‘yanuwa da danginsa, har da maid akin da marigayin (Dagacin), ya bari.”

Kara karanta wannan

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

Amma an yi sa’a, sun fito da mutane hudu daga cikin wadanda suka dauka, sai dai kuma sun rike bazawararsa. Har yanzu da nake magana, tana hannunsu.”

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda na Katsina, SP Gambo Isah, ya ce zai yi magana da DPO na sashen da ake zargin abin ya faru, domin jin yadda aka yi.

A baya an ji Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari yace kananan hukumomi 10 cikin 34 na jiharsa na fuskantar munanan hare-hare a kullum daga 'yan bindiga.

Gwamna Masari ya bayyana haka ne yayin da karbi bakuncin babban hafsan sojin kasa. Daga baya an ji gwamnan ya na kira ga mutanensa, su tashi, su kare kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng