Harin yan bindiga kan makarantar sojoji abun kunya ne – Kungiyar ACF

Harin yan bindiga kan makarantar sojoji abun kunya ne – Kungiyar ACF

  • Kungiyar ACF ta yi martani a kan harin da ‘yan bindiga suka kaiwa Kwalejin horon sojoji na Najeriya (NDA)
  • Kungiyar arewar ta bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki
  • Ta kuma nemi a ceto jami'in da aka sace tare da gurfanar da masu laifin

Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta nuna bacin ranta game da harin da ‘yan bindiga suka kaiwa Kwalejin horon sojoji na Najeriya (NDA), Daily Nigerian ta ruwaito.

Da sanyin safiyar Talata, 24 ga watan Agusta ne wasu 'yan bindiga sun kai hari a makarantar sannan kuma suka kashe jami'anta biyu, inda suka yi garkuwa da daya a cikin lamarin.

Harin NDA: Akwai gagarumin matsala a tsarin tsaron kasarmu - ACF
Kungiyar ACF ta nuna bakin ciki a kan harin da 'yan bindiga suka kai NDA Hoto: The Punch
Asali: UGC

Da take mayar da martani a cikin wata sanarwa da kakakinta, Emmanuel Yawe ya fitar, ACF ta ce abin bakin ciki ne cewa "'yan fashin titi" za su iya mamaye NDA.

Kara karanta wannan

Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara

Yawe ya ce dole ne a ceto jami'in da aka sace sannan a gurfanar da wadanda suka kai harin, jaridar TheCable ta ruwaito.

Ya ce:

“Wadannan manyan jami’ai sun yi gagarumin sadaukarwa ga Najeriya, kasarsu ta asali.
"Muna fatan sadaukarwar su ba ta banza ba ce. Kungiyar tana addu’a don ganin cewa an kubutar da jami’in da aka sace tare da gurfanar da masu laifin da suka sace shi.
“Abin takaici ne ƙwarai da gaske cewa ‘yan fashin titin kawai za su mamaye wani sansanin soji na irin wannan babban martaba na ƙasa da ƙasa, su mamaye tsarin tsaro da jami’ai a wurin, su kashe jami’an sannan su tafi da ɗaya zuwa inda ba a sani ba.
“NDA abin tunawa ne mai cike da alfahari da nasarorin da kakanninmu suka samu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

“Mu a ACF mun sha nanatawa cewa akwai matsala game da gudanarwar tsaronmu. A kwanakin baya wasu da ake kira 'yan fashi ne suka harbo wani jirgin yakin sojin saman Najeriya.
“A yau masana’antar da ake samar da dukkan hafsoshin sojojin Najeriya an mamaye ta an lalata ta. Me kuma muke bukata don nuna cewa tsarin tsaronmu na kasa yana aiki ne a baya?”

NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

A baya mun kawo cewa makarantar horar da Sojin Najeriya (NDA) ta tabbatar da kisan jami’ai biyu a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari barikin a ranar Talata, 24 ga watan Agusta.

Sanarwar da jami'in hulda da jama'a na makarantar, Manjo Bashir Jajira ya fitar, ya ce 'yan bindigar sun sace wani jami'i, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

NDA ta bayyana cewa tana kan bin diddigin 'yan fashin da suka yi kutse a tsarin tsaronta, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Majalisar Dinkin Duniya ta tono sirrin Gwamnatin Tarayya wajen kawo karshen yakin Boko Haram

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng