Gwamnoni Sun Aike da Muhimmin Sako Ga Gwamna Zulum Kan Kyakkyawan Jagorancinsa

Gwamnoni Sun Aike da Muhimmin Sako Ga Gwamna Zulum Kan Kyakkyawan Jagorancinsa

  • Kungiyar gwamnonin APC ta aike da sakon taya murnar ranar haihuwa ga gwamna Babagana Umaru Zulum
  • Gwamnonin sun bayyana cewa Zulum na taka muhimmiyar rawa wajen yaki da matsalar tsaro a faɗin Najeriya
  • A ranar 26 ga watan Agusta, 2021, Gwamnan Zulum ya cika shekara 52 a duniya

Borno - Kungiyar gwamnonin APC (PGF), ranar Alhamis ta jinjinawa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, bisa abinda ta kira kyakkyawan jagoranci da yake gudanarwa, kamar yadda punch ta ruwaito.

Wannan na kunshe a cikin wani sako mai taken, "Sakon taya murnar ranar haihuwa ga mai girma Farfesa Babagana Umaru Zulum."

Sakon na ɗauke da sa hannun shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, wanda aka fitar a Abuja.

Gwamnan Borno, Babbagana Zulum
Gwamnoni Sun Aike da Muhimmin Sako Ga Gwamna Zulum Kan Kyakkyawan Jagorancinsa Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Kungiyar PGF ta kunshi dukkan gwamnonin da aka zaɓa karkashin inuwar jam'iyyar APC a faɗin kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muna tayaka murna da dukkan iyalanka

Wani sashin sakon gwamnonin yace:

"Muna taya mai girma gwamna murnan zagayowar wannan rana mai muhimmanci, iyalanka da kuma al'ummar jihar Borno baki ɗaya."
"Muna jinjina gare ka bisa jagorancinka wanda ya kasance abin koyi, kyawawan kudirorinka da kokarinka na haɗa kai da kawo zaman lafiya a Najeriya."
"Karkashin jagorancin jam'iyyar mu APC, da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kana taka muhimmiyar rawa wajen yaki da Boko Haram a arewa maso gabas da matsalar tsaro a sassan Najeriya."

Zamu cigaba da aiki tare domin kawo cigaba

Gwamnonin sun bayyana cewa suna taya mai girma gwamna, Farfesa Babagana Umaru Zulum murnar wannan rana, kamar yadda vangaurd ta ruwaito.

Hakanan kuma gwamnonin sun jaddada cewa a shirye suke a ɗora daga inda aka tsaya wajen haɗa karfi-da-karfe tare da gwamnatin tarayya karkashin shugaba Buhari, a aiwatar da shirye-shiryen da zasu amfani al'umma.

A cewar gwamnonin zasu cigaba da aiki tare domin samar da ayyukan yi, yaki da matsalar tsaro, farfado da tattalin arziki da kuma kawar da talauci tsakanin yan Najeriya.

A wani labarin kuma Mutum 16 Sun Mutu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Ragargaji Mayakan Boko Haram 50 a Nijar

Mayakan Boko Haram sun kai hari kudu maso gabashin Nijar dake fama da hare-haren masu ikirarin jihadi.

Ministan tsaron kasar yace an kashe sojoji 16 tare da jikkata wasu mutum 9 yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel