Sabanin saki cikin fushi, ma'aurata sun yi shagalin rabuwa da juna cikin farin ciki

Sabanin saki cikin fushi, ma'aurata sun yi shagalin rabuwa da juna cikin farin ciki

  • Wata mata ‘yar kasan Uganda Nantogo Immaculate ta yi farin cikin mutuwar aurenta, abun da mutane da dama kan bar wa zuciyarsu
  • A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa an dauki tsawon shekaru shida kafin a bata sakin amma daga karshe ya faru ya kare
  • Ta kuma kara da cewa ita da tsohon mijinta sun ci abincin karshe tare kafin kowa ya kama gabansa a hukumance

Sabanin labarai da yawa na ma'aurata da ke rabuwa cikin baran-baran cikin tashin hankali, Nantongo Immaculate ta yi farin ciki da mutuwar aurenta.

Mata ta yi murnar mutuwar aurenta shekaru 6 bayan rabuwa, ta ci abincin karshe tare da tsohon mijin nata
Immaculate Nantongo ta ci abincin karshe tare da tsohon mijin nata Hoto: Immaculate Nantongo
Asali: UGC

Cincin din murnar mutuwar aure

A cikin abin da ta kira a matsayin dakatar da kyamar kisan aure, ta wallafa hotunanta da tsohon mijinta suna cin abinci, da kuma wani cincin din “murnar rabuwar aure.”

Ta kara da cewa su biyun sun hadu ne domin murnar kawo karshen tarayyar da ya haifar da kyawawan yara maza biyu, gami da abokantaka, renon yara tare, da sanin yakamata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta rubuta a Facebook:

"Shekaru bakwai da suka gabata ban san za mu kasance a wannan wuri zaune tare muna cin abinci tare ba. Yadda lokaci ke warkar da komai."

Immaculate ta yi hanzarin lura da cewa motsin zuciyarta ba ta da niyyar nuna kyama ga mutuwar aure amma yana ƙarfafa sauran mutane da ke cikin irin wannan yanayin gwiwa domin rungumar abubuwan da ke faruwa.

Ba ƙarshen rayuwa ba kenan

A matsayinta na wacce ya faru da ita,ta sake nanata cewa mutuwar aure ba shine ƙarshen rayuwa ba kuma tsoffin ma’aurata na iya mu’amalla mai kyau.

Ta ce:

"Rayuwa na iya ci gaba da zama mai kyau, amma kuma don sanar da ku cewa Allah baya fushi da ku. Ee, baya son mutuwar aure amma yana son ku sosai."

A cewarta, babu wani mahaifi da zai yi farin ciki da sanin cewa ɗansu yana jure wa mummunan alaƙa, wanda ta ke nufin cewa ko Allah yana fahimtar lokacin da mutane ke raba hanya.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sanda sun damke mahaifiyar da ta garkame tare da hana dan ta abinci

Renon yara tare

Immaculate ta bayyana cewa Allah yana ƙin mutuwar aure saboda abin da yake yiwa mutane, domin yana raba iyalai.

Sai dai, ta yi imanin cewa a tsakiyar mutuwar aure mutum na iya zaɓar yin abin da ya fi dacewa daga halin da ake ciki, musamman kula da yara tare.

Ta ce:

"Abu ne da ya shafi baiwa yaranku dama mafi kyawu a rayuwa. Yanke shawara mafi kyau a gare su."

A kan wannan yanayin ne masoya a baya suka hadu a karo na ƙarshe don murnar rayuwar da suka yi da rayuwar da za su yi a yanzu.

Ta taƙaita komai a matsayin “Ranar murnar rabuwar aure” da kuma jefar da komai zuwa babi na gaba na rayuwarta.

Hotuna da bidiyon kasaitaccen bikin mutuwar aure da wata yar Najeriya tayi

A baya mun kawo cewa wata yar Najeriya, Ikea Bello, ta yi fice a kafafen sada zumunta bayan ta yi wani abin da ba a saba gani ba.

Kara karanta wannan

Garin Dadi: Kasar turai, inda za ka iya sayen katafaren gida a kasa da N500

Kwararriyar mai koyar da rayuwar ta yi bikin mutuwar aurenta cikin kasaita.

Ta yi gagarumin liyafa yayin da take murnar samun yancinta tare da abokai da masu fatan alheri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel