Atiku ya tura sako ga PDP, ya ce duk rintsi a kwace mulki a hannun Buhari a 2023

Atiku ya tura sako ga PDP, ya ce duk rintsi a kwace mulki a hannun Buhari a 2023

  • Atiku Abubakar ya tura babban sako ga jam'iyyar PDP kan batun tsayawa takararsa 2023
  • Ya bayyana godiya da kuma yabo ga dukkan mambobin jamiyyar ta PDP a matakin kasa
  • Hakazalika, Atiku ya bukaci 'yan Najeriya su hada kai wajen dawo da martabar Najeriya

Abuja - Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya aika sako ga shugabancin jam'iyyar PDP gabanin zaben shugaban kasa mai zuwa a kasar a shekarar 2023.

Takardar an ce bayyana alama ce ta farko na sake nuna sha’awar Atiku Abubakar na neman tikitin takarar shugaban kasa na 2023 na jam’iyyar adawar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Atiku, bai bayyana ko zai nemi wani matsayi a yakin neman zaben shugaban kasa ba a cikin sakon mai kwanan wata 29 ga Yuni, 2021 ba.

Kara karanta wannan

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

Legit.ng ta tattaro cewa jaridar ta ce, Ripples Nigeria, wacce ta fara wallafa abubuwan da ke cikin sakon a ranar Asabar, 21 ga watan Agusta, ta lura cewa batun tsohon mataimakin shugaban kasar ga jam’iyyarsa don nuna sha’awarsa ta shiga jerin 'yan takarar 2023.

Babbar magana: Atiku ya tura sako ga PDP, ya ce duk rintsi a hambarar da APC a 2023
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar | Hoto: guardian.ng
Asali: Facebook

A cewar rahoton, Atiku, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na 2019 na PDP, ya nuna godiya ga membobin jam’iyyar kan goyon bayan da aka ba shi a lokacin zaben 2019, yana mai lura da cewa a yanzu jam’iyyar za ta fi samun ingantacciyar nasarar lashe zaben 2023.

Wane hali Najeriya ke ciki?

An kuma ambato Atiku a cikin bayanin cewa a halin yanzu Najeriya tana cikin matukar bukatar kulawa kuma ya bukaci PDP da ta hada kai dashi wajen warkar da kasar ta hanyar sabon tsarin siyasa da tattalin arziki wanda zai haifar da sake dawo da tsarin mulkin kasa.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa na cika da bakin ciki da nadama, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya magantu

A cewar The Nation, sashin sakon na cewa:

“Cikin matukar girmamawa nake isar muku, babbar godiyata da yabo ga dimbin goyon baya da dimbin kuri’un zaben da aka kada don tallafawa jam’iyyar mu ta PDP, da takarar ta na shugaban tarayyar Najeriya a babban zaben 2019.
"Yanzu, muna da mafi kyawun kayan aiki, kuma dole ne dukkan 'yan uwanmu su hada kai a yau don samar da sabon tsarin siyasa da tattalin arziki wanda ya kamata ya sake inganta kasar mu abin kaunarmu
"Mun shirya tsaf don yin aiki tare wajen dawo da fata, janye Najeriya daga kangi da kuma rayar da kishin kasa na kakanninmu! Na yi imanin cewa tare za mu sake gina shingayen mu, mu gyara katangun mu da suka fashe, mu dawo da fata, mu dawo da Najeriya kan tafarki mai girma. Tabbas, zamu iya, kuma dole ne. ”.

A tattaunawarsa da jaridar, mai ba Atiku shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya tabbatar da sahihancin sakon.

Kara karanta wannan

2023: Yemi Osinbajo ya bayyana abin da zai faru da APC bayan Shugaba Buhari ya bar mulki

Sai dai, ya yi watsi da jita-jitar cewa sakon sanarwa ce ta uban gidan nasa na neman tsayawa takara a 2023.

An cimma nasara: Minista Pantami ya ce saura kiris 5G ya fara aiki a Najeriya

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da jimawa ba za ta dasa cibiyar sadarwa ta 5G a cikin kasar don kara gudun cudanyar yanar gizo, in ji TheCable.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani Isa Pantami ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

Pantami ya ce shawarar dasa cibiyar sadarwa ta 5G ta biyo bayan sakamakon cikakken bincike, kwakwaf da gwajin kawar shakku kan barazana ga tsaro ko kiwon lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel