Da dumi-dumi: Hawaye sun kwaranya yayin da tsohon sanatan Najeriya ya mutu
- Najeriya ta rasa daya daga cikin fitattun masu ruwa da tsaki a harkar siyasa, Sanata Biyi Durojaye, tsohon dan majalisar tarayya
- Sanata Durojaye wanda ya kuma kasance tsohon shugaban kwamitin kwamishinonin hukumar NCC ya rasu da sanyin safiyar Talata, 24 ga watan Agusta, bayan gajeriyar rashin lafiya
- Iyalinsa sun tabbatar da mutuwar, tare da bayyana cewa nan ba da jimawa ba za su sanar da lokacin da za a karɓi ziyarar ta'aziya tare da la'akari da cutar ta COVID-19
Lagos, Najeriya - Dan majalisar jamhuriya ta hudu, Sanata Biyi Durojaye, ya mutu, a cewar wani rahoto da The Nation ta gabatar a ranar Talata, 24 ga watan Agusta.
Jaridar ta ambato wasu majiyoyi na cewa Durojaye ya mutu da sanyin safiyar Talata, 24 ga watan Agusta a Legas yayin da yake samun kulawar likita.
An tattaro cewa Durojaiye, mai shekaru 88, ya taba rike mukamin shugaban kwamitin kwamishinonin hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC).
A halin da ake ciki, wata sanarwa da dangin mamacin suka aikewa Legit.ng ta kuma tabbatar da ci gaban.
Sanarwar tana cewa:
"Tare da godiya ga Allah da mika kai ga nufinsa, muna sanar da mutuwar ubanmu, kakanmu, babban kakanmu, dan'uwanmu, kawunmu, dan uwanmu kuma abokinmu, Sanata Olabiyi Durojaiye.
"Ya koma ga Ubangiji da sanyin safiyar Talata, 24 ga watan Agusta 2021, bayan gajeriyar rashin lafiya a lokacin da ya cika shekaru 88.
"Iyalan za su ba da sanarwar lokacin da aka yi shirye -shiryen da suka dace daidai da ƙa'idodin korona don karɓar ziyarar ta'aziyya."
Matar tsohon Shugaban Ƙasar Nigeria na mulkin Soja, Aguiyi Ironsi, ta rasu
A gefe guda, Victoria Aguiyi-Ironsi, matar marigayi tsohon shugaban kasan mulkin soji na Nigeria, Manjo Janar Johnson Aguiyi-Ironsi, ta mutu, The Guardian ta ruwaito.
Tsohuwar first lady din ta rasu ne a ranar Litinin tana da shekaru 97 a duniya.
Za ta cika shekaru 98 a ranar 21 ga watan Nuwamban 2021.
Asali: Legit.ng