Da Dumi-Dumi: Shugaban Jam'iyyar PDP, Adegbola Dominic, Ya Rigamu Gidan Gaskiya
- Shugaban babbar jam'iyyar adawa PDP, reshen jihar Lagos, Adegbola Dominic, ya kwanta dama
- Kakakin jam'iyyar na jihar, Taofeeq Gani, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba
- Yace za'a sakko da tutocin PDP dake faɗin jihar Lagos zuwa rabi domin nuna alhinin mutuwarsa
Lagos - Shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Lagos, Adegbola Dominic, ya kwanta dama, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Kakakin PDP na jihar, Taofeeq Gani, shine ya tabbatar da mutuwar ga wakilin Punch ta wayar salula.
Gani ya bayyana cewa shugaban PDP na jihar Lagos ya mutu ranar Laraba da yamma bayan fama da cutar da ta shafi COVID19.
Cutar Korona ta yi ajalin shugaban PDP
A wani jawabi da ya fitar, Gani yace:
"Shugaban PDP na jihar Lagos ya mutu bayan fama da cutar COVID19, Marigayin wanda babban ma'aikacin lafiya ne, ya kasance ɗan siyasa na daban wanda ya amince da zuba mafi yawan kuɗinsa a hanyar da mutane zasu ji daɗi."
"Kafin mutuwarsa Dakta Dominic, shine shugaban asibitin Santa Maria.Ya rike mukamai da dama a tarihin siyasarsa."
"Marigayin ya rike ofishin SDF na jiha, shugaban PAC na jiha, Shugaban jam'iyyar PAN ta ƙasa, da shugaban jam'iyyar PDP ta jihar Lagos."
Wace kujerar mulki ya rike?
Gani ya kara da cewa ya taba tsayawa takarar gwamnan jihar Lagos karkashin inuwar jam'iyyar APGA.
Hakanan shine ɗan takarar kungiyar Jakande a lokacin zaɓen fidda gwani na jam'iyyar SDP a kujerar sanatan Lagos ta yamma, inda ya fafata da Bola Tinubu.
Bugu da kari, Gani yace a koda yaushe burin marigayi Dominic shine cigaban jihar Lagos kuma tabbas zai yi dana sanin barin jihar ba yadda yaso ba.
Za'a sauke tutocin PDP a Lagos zuwa rabi
Mista Gani yace za'a jima ba'a manta da marigayi Adegbola Dominic a siyasar jihar Lagos ba, kamar yadda the nation ta ruwaito.
"Muna mika ta'aziyyar mu ga iyalansa. Za'a sauke dukkanin tutocin PDP zuwa rabi kuma duk wani taron PDP a wannan lokacin zai kasance addu'a ce gare shi."
A wani labarin kuma PSG Ta Yi Watsi da Makudan Kudin da Real Madrid Ta Saka Wa Mbappe, Harry Kane Ya Bayyana Makomarsa
PSG ta yi watsi da tayin Real Madrid na dala miliyan $188m don ɗaukar ɗan wasa Kylian Mbappe. Daraktan wasanni na PSG yace kungiyar ba zata siyar da ɗan wasa a wannan kuɗin ba
Harry Kane na Tottenham ya bayyana cewa bai shirya barin kungiyar da yayi wayo a cikinta ba.
Asali: Legit.ng