PSG Ta Yi Watsi da Makudan Kudin da Real Madrid Ta Saka Wa Mbappe, Harry Kane Ya Bayyana Makomarsa

PSG Ta Yi Watsi da Makudan Kudin da Real Madrid Ta Saka Wa Mbappe, Harry Kane Ya Bayyana Makomarsa

  • PSG ta yi watsi da tayin Real Madrid na dala miliyan $188m don ɗaukar ɗan wasa Kylian Mbappe
  • Daraktan wasanni na PSG yace kungiyar ba zata siyar da ɗan wasa a wannan kuɗin ba
  • Harry Kane na Tottenham ya bayyana cewa bai shirya barin kungiyar da yayi wayo a cikinta ba

Madrid, Spain - Kungiyar PSG ta kasar Faransa ta yi fatali da tayin Real Madrid a kokarinta na ɗaukar ɗan wasan gaba, Kylian Mbappe ranar Laraba, kamar yadda punch ta ruwaito.

Daraktan wasanni na PSG, Leonardo, yace tayin Real na kimanin $188 million "Yayi kaɗan" a kan ɗan wasan da suke son "Ya zauna a PSG."

Daraktan yace:

"Bukatar mu a koda yaushe shine Kylian ya zauna tare da mu a PSG, ya sabunta kwantiraginsa da mu, wanda zai kare a watan Yuni mai zuwa."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Abokin Atiku Ya Yi Watsi Da Shi, Ya Faɗi Ɗan Takarar Da Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

Kylian Mbappe
PSG Ta Yi Watsi da Makudan Kudin da Real Madrid Ta Saka Wa Mbappe, Harry Kane Ya Bayyana Makomarsa Hoto: completesports.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma bayyana tayin da Real Madrid ta yiwa ɗan wasan wanda ya lashe kofin duniya da kasarsa ta Faransa a matasyin "Cin mutunci, bai dace ba kuma ya saba wa doka."

Leonardo ya kara da cewa idan ɗan wasan mai shekara 22 yana son barin kungiyar babu wanda zai rikesa, amma "zai tafi ne ko ya zauna a kan sharuddan mu."

Nawa PSG ta sayi Mbappe daga Monaco?

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa PSG ta lalewa Monaco zunzurutun kudi Yuro miliyan 180 domin raba ta da ɗan wasan a 2017, kuma a shirye take ta sabunta zamansa.

Tun bayan komawar Messi PSG, shugaban ƙungiyar, Nasser Al-Khelaifi, yace Mbappe ba shi da wani zaɓi illa ya zauna a PSG.

Zan cigaba da zama a Tottenham - Kane

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Kara Kaɗa Hanjin PDP Kan Wanda Ya Dace Ya Gaji Buhari a 2023

Ɗan wasa gaba na kungiyar Tottenham ta kasar Ingila ya kawo karshen raɗe-raɗin tafiyarsa Man City ranar Laraba.

Kane, ɗan kimanin shekara 28, ya bayyana cewa yana nan daram a kungiyarsa ta Tottenham, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Ɗan wasan gaban ya bayyana a fili cewa ba shi da kudirin barin kungiyar da ya taso tun yana karamin yaro.

Kane shine na biyu a jerin yan wasan da suka fi zurawa Tottenham kwallo a raga a tarihi amma har yanzun bai taɓa cin wata gasa da kungiyar ba.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dalibar Wata Jami'a, Su Nemi a Tattaro Miliyoyi Kudin Fansa

Wasu miyagun yan bindiga sun sace ɗalibar jami'ar jihar Kwara, dake karatun jarida.

Maharan sun tuntubi hukumar jami'ar, inda suka nemi a tattara musu miliyan N50m kuɗin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel