Yanzu-Yanzu: An kashe mutane masu yawa, an yi ƙone-ƙone yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos

Yanzu-Yanzu: An kashe mutane masu yawa, an yi ƙone-ƙone yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos

  • Wani sabon rikici ya sake barkewa a karamar hukumar Jos ta Arewa, jihar Plateau
  • Wani mazaunin Yelwan Zangam, Yakubu Bagudu ya tabbatar da barkewar rikicin
  • Bagudu ya ce an kashe a kalla mutane 30, sannan an kona gidaje da dama a garin

Jihar Plateau - An ruwaito cewa an kashe mutane da dama a garin Yelwan Zangam da ke karamar hukumar Jos ta Arewa na Jihar Plateau.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kuma kone gidaje masu yawa yayin harin.

Yanzu-Yanzu: An kashe mutane masu yawa yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos
Yanzu-Yanzu: An kashe mutane masu yawa yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos
Asali: Original

Wannan na zuwa ne kimanin sati daya bayan kashe matafiya 27 a hanyar Gaba-biyu-Rukuba a karamar hukumar Jos din ta Arewa.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa

Yakubu Bagudu, wani mazaunin yankin ya tabbatarwa Daily Trust afkuwar wannan harin a safiyar ranar Laraba.

Ya ce an kashe kimanin mutane 30, ya kara da cewa an turo jami'an tsaro zuwa yankin.

Daily Trust ba za ta iya tabbatar da adadin mutanen da aka kashe ba yayin harin.

Rundunar yan sandan jihar Plateau ba ta riga ta fitar da sanawarwa game da harin ba a lokacin hada wannan rahoton.

Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa

An kama mutane 10 da suke da alaka da kai sabon harin kauyen Yelwa Zangam na Jos ta arewa da ke jihar Filato, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Gwamna Simon Lalong ya kwatanta harin a matsayin rashin imani, sannan ya shirya taro na gaggawa don tattaunawa da kuma neman hanyar kawo garanbawul ga kashe-kashen da aka maimaita a jiharsa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan kisan mutune, Gwamnan Plateau ya sake kakaba dokar ta baci ba dare ba rana

A wata takarda wacce darektan watsa labarai ya saki, Makut Mechan, ya ce gwamnan ya umarci jami’an tsaro su binciko duk wadanda suke da hannu a lamarin da masu daukar nauyinsu don a hukunta su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel