Baku San Abinda Kuke Yi Ba, Tsohon Sarkin Ƙano Sanusi II Ya Yi Magana Kan Raba Najeriya

Baku San Abinda Kuke Yi Ba, Tsohon Sarkin Ƙano Sanusi II Ya Yi Magana Kan Raba Najeriya

  • Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, yace sam baya goyon bayan a raba Najeriya
  • Khalifa Sanusi ya bayyana cewa waɗanda suke fafutukar ɓallewa daga Najeriya basu san illar abinda suke aikatawa ba
  • Sanusi yace kamata yayi su jingine tunaninsu, su zo a haɗa karfi wajen magance duk wasu kalubale

Abuja - Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, yace baya goyon bayan masu fafutukar a raba Najeriya, kamar yadda punch ta ruwaito.

Sanusi ya yi wannan magana ne a wurin taron kaddamar da littafinsa ranar Talata a Lagos.

An kaddamar da littafin ne a wani ɓangare na bikin murnar ciksarsa shekara 60 a duniya da kuma tattara kuɗaɗe don tallafawa ilimin 'ya'ya mata.

A cewar Sanusi, Khalifan Tijjaniyya a Najeriya, duk masu fafutukar ballewa daga Najeriya ba su san abinda suke aikatawa ba.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dalibar Wata Jami'a, Sun Nemi a Tattaro Miliyoyi Kudin Fansa

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II, a wurin taron kaddamarwa
Baku San Abinda Kuke Yi Ba, Tsohon Sarkin Ƙano Sanusi II Ya Yi Magana Kan Raba Najeriya Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Khalifa Sanusi yace:

"Ina fatan abinda nake tunani shine a ran kowa dake nan, dole mu dunkule wuri ɗaya, waɗanda suke bukatar a raba kasar nan basu san abinda suke yi ba."
"Ƴa kamata mu cigaba da zama tsintsiya ɗaya, idan mun yi korafi kan wani abu, mun yi hakan ne domin muna kaunar Najeriya."
"Fatan mu shine kowa ya bada gudummuwarsa, har da waɗanda suka jefa kansu cikin waccan hanya mai wahala, domin kawo cigaba a kasar mu."

Zamu cimma nasara da dama a dunkule

Tsohon gwamnan CBN ya jadadda cewa Najeriya zata ɗaga sama matukar ta cigaba da zama a dunkule, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya roki yan Najeriya su daina jiran sai gwamnati ta warware musu dukkan matsalolin su, amma su haɗa kai wajen tallafa wa gwamnati ta warware kalubalen da take fama da shi.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II, Ya Magantu Kan Kudirin FG Na Zare Tallafin Man Fetur da Wutar Lantarki

Mu haɗa hannu wajen tallafawa 'ya'ya mata su samu ilimi

Khalifan ya kaddamar da littafinsa a wurin taron da nufin tattara kuɗin da za'a yi amfani da su wajen tallafawa ilimin 'ya'ya mata.

Ya koka cewa akwai yara mata da yawan gaske da suka kammala sakandire amma ba su da kuɗin da zasu cigaba da zurfafa iliminsu.

Sanusi yace za'a cigaba da haɗa kuɗaɗen kuma ana fatan tara dalar Amurka miliyan biyu cikin shekara 5 domin tallafawa ɓangaren ilimin mata.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sace Sakataren Hukumar Zaɓe a Jihar Nasarawa

Yan bindiga da ba'a san su ba sun sace sakataren hukumar zaben jihar Nasara (NASIEC), Barista Muhammad Abubakar.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin gidan sakataren da daren ranar Talata, kuma suka tafi daashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262