Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II, Ya Magantu Kan Kudirin FG Na Zare Tallafin Man Fetur da Wutar Lantarki
- Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, yace cire tallafin man fetur da na lantarki kusan ya zama wajibi
- Sanusi yace ba zai yuwu kasar nan ta cigaba da ciyo ba shi ba yayin da za'a barwa mutanen gobe alhakin biya
- Sanusi, wanda shine Khalifan Tijjaniyya, yace yan Najeriya su daina ɗora alhakin komai a kan gwamnati
Abuja - Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya yi kira ga yan Najeriya su shirya su fara tunanin abinda zasu yi domin tallafa wa kansu maimakon dora komai kan gwamnati, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Sanusi, wanda shine khalifan tijjaniyya a Najeriya, ya faɗi haka ne a wurin taron bikin da aka shirya domin murnar cikarsa shekara 60 a duniya.
Tsohon sarkin yace:
"Ya kamata yan Najeriya su fahimci cewa hanyar da muka biyo ba mai ɓullewa bace. Ba zai yiwu gwamnati ta cigaba da biyan tallafin fetur ba."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Yan Najeriya su lura da cewa tsarin da muka ɗakko na tafiyar da mulkin kasar nan ba zai cigaba a haka ba. Ba zamu cigaba da tallafin man fetur ba, haka kuma ba zamu cigaba da tallafin wutar lantarki ba."
Ta ya zamu lalata goben kasar nan?
Sanusi ya kara da cewa ya zama wajibi a nemi hanyar da za'a daina dogara da ciyo bashi, don lamarin na lalata goben kasar nan.
"Waɗannan tallafin abu ne da muke bukata amma ba zamu iya jurewa ba. Amma fa sai mun yi wannan sadaukarwar."
"Idan muka ki yi a yanzun, muka sa hanyoyin samun kuɗin gwamnati ya dogara kacokan a kan ciyo ba shi, to muna jefa goben kasar nan cikin mummunan hatsari."
"Zamu cigaba da tara bashi yayin da zamu tura alhakin biyan bashin kan al'ummar gobe. Wajibi mu yi karatun ta natsu, mu ɗauki matakin da ya dace."
Mu daina dogaro da gwamnati kan komai
Sanusi ya bayyana cewa yan Najeriya suna bata wa kansu lokaci ne idan suka tsaya jiran gwamnati ta magance musu kowace matsala dake damun su.
A cewarsa wannan ƙalubalen da ake fuskanta na samar da cigaba, kowa ya tambayi kansa mezan iya yi a karan kaina?
A wani labarin kuma Na Samar da Isasshen Fasahar Zamani da Za'a Magance Matsalar Tsaro, Sheikh Pantami
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dakta Isa Pantami, yace ya yi bakin kokarinsa wajen samar da isashen fasahar zamani da zai taimaka wa hukumomin tsaro su magance matsalar tsaro a faɗin kasar nan.
Ministan yace duk abinda hukumomin tsaro suka bukata daga ɓangarensa yana samar musu ɗari bisa ɗari, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng