Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sace Sakataren Hukumar Zaɓe a Jihar Nasarawa

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sace Sakataren Hukumar Zaɓe a Jihar Nasarawa

  • Wasu yan bindiga da ba'a san su ba sun yi awon gaba da sakataren hukumar zaɓe ta jihar Nasara, Barista Muhammad Abubakar
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin gidan sakataren da daren ranar Talata, kuma suka tafi daashi
  • Kwamishinan yan sandan jihar Nasarawa ya ɗauki matakin gaggawa domin kubuyar da sakataren da kame maharan

Nasarawa - Yan bindiga da ba'a san su ba sun sace sakataren hukumar zaben jihar Nasara (NASIEC), Barista Muhammad Abubakar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, ASP Rahman Nansel, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Lafia, babban birnin Nasarawa.

Yan bindiga sun sace sakataren NASIEC
Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sace Sakataren Hukumar Zaɓe a Jihar Nasarawa Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya bayyana cewa maharan akalla su biyar sun farmaki gidan sakataren NASIEC, dake kauyen Bakin Rijiya, kan hanyar Lafia zuwa Shendam da misalin karfe 11:45 na daren Talata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An kashe mutane masu yawa, an yi ƙone-ƙone yayin da sabon rikici ya ɓarke a Jos

Yan bindigan sun sami nasarar awon gaba da shi zuwa wani uwri da ba'a sani ba, a cewar jawabin kakakin yan sandan, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Jawabin yace:

"Ranat 25 ga watan Agusta an shigar da kara ofishin yan sanda na Lafia cewa wasu mahara akalla 5 sun kai hari gidan sakataren NASIEC dake kauyen Bakin Rijiya, sun tafi da shi."

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa bayan samun wannan rahoton ne kwamishinan yan sanda, CP Adesina Soyemi, ya tada tawagar jami'an yan sanda cikin gaggawa zuwa wurin da ake zargin maharan na tsare da wanda suka sace.

ASP Nansel yace an umarci mataimakin kwamishinan yan sandan jihar, mai kula da sashin binciken kwakkwafi na manyan laifuka ya gudanar da bincike kan lamarin, domin kubutar da sakataren da kame maharan.

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 da ya kamata ka sani game da harin da yan bindiga suka kai NDA

Ya yi kira ga al'ummar jihar su taimakawa jami'an tsaro da bayanai, wanda zai saukaka musu aikinsu, a kuɓutar da wanda aka sake sannan a kame maharan.

NASIEC zata gudanar da zaɓe

Hukumar NASIEC ta sanar da cewa zata gudanar da zaɓe a kananan hukumomi 13 na jihar domin cike gurbi kujerun shugabanni da kansiloli a ranar 6 ga watan Oktoba.

A wani labarin kuma Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II, Ya Magantu Kan Kudirin FG Na Zar Tallafin Man Fetur da Wutar Lantarki

Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, yace cire tallafin man fetur da na lantarki kusan ya zama wajibi.

Sanusi yace ba zai yuwu kasar nan ta cigaba da ciyo ba shi ba yayin da za'a barwa mutanen gobe alhakin biya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel