Yadda 'yan bindiga suka sace ɗalibin NDA kuma ɗan alƙali a Kaduna

Yadda 'yan bindiga suka sace ɗalibin NDA kuma ɗan alƙali a Kaduna

  • Wani majiya ya bayyana abubuwan kunya da suka faru a NDA gabanin harin da yan bindiga suka kai a baya-bayan nan
  • A cewar majiyar, masu garkuwa sun taba sace wani dan babban alkali kwanaki kada kafin ya gama NDA
  • Majiyar ya kara da cewa sai da aka biya kudin fansa kafin masu garkuwar suka sako dan alkalin

Jihar Kaduna - Harin da yan bindiga suka kai gidajen Makarantar Bada Horon Aikin Soja na Kaduna, NDA ya janyo cece-kuce a tsakanin mutane a kasar kan lamarin tabarbarewar tsaro.

NDA, jami'ar bada horaswar aikin soja da ke Kaduna ce ke horas da dakaru na rundunar sojojin kasa, sojojin sama da sojojin ruwa.

Baya ga karatutuka na gaba da digiri na farko da ake yi a jami'ar, tana kuma yin kwasa-kwasai na musamman masu alaka da aikin soja da tsaro daga kasashen da ke makwabtaka da Nigeria.

Kara karanta wannan

Afghanistan: Wata kungiya ta bullo domin kalubalantar mulkin Taliban, ta harba makami

Yadda 'yan bindiga suka sace ɗalibin NDA kuma ɗan alƙali a Kaduna
Jami'ar Bada Horaswar Aikin Soja ta NDA a Kaduna. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar Talata ne yan bindiga suka kutsa jami'an suka halaka jami'ai biyu suka sace daya mai mukamin manjo.

Bayan afkuwar hakan, wata majiya daga rundunar sojoji ta shaidawa Daily Trust wasu ababen ban kunya da suka faru a NDA da wasu hukumomin soji.

Majiyar ta ce ya kamata mahukunta su dauki matakin dakile abin cikin gaggawa.

An biya kudin fansa kafin aka sako dalibin NDA kuma dan alkali da aka sace

A cewar majiyar:

"Kimanin shekaru biyu da suka gabata, yan bindiga sun sace wani dalibin soja kwanaki kadan kafin yaye su daga NDA."
"Dan wani alkali ne daga daya daga cikin jihohin Arewa maso tsakiya ... sai da aka biya kudin fansa kafin aka sako shi."

Masu tsaron kofofin shiga NDA suna sakaci

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

Wata majiyar ta shaidawa Daily Trust cewa shiga NDA ba wani abu bane mai wahala saboda ba a tsananta bincike a kofofin shiga.

Ya ce:

"Ba sa yin binciken da ya dace, wasu lokutan suna tambaya ko kai wanene amma mafi yawanci ba su tambayan. Hakan yasa mutane daban-daban ke iya shiga wuri na soji kamar NDA"

Wani majiyar ya ce sansanin yan bindigan ba shi da nisa daga jami'ar ta NDA don haka ya ke mamakin abin da yasa ba a tafi an tarwatsa su ba.

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Sace Sakataren NASIEC a Nasarawa

A wani labarin daban, Ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace Mohammed Okpu, sakataren Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Jihar Nasarawa, The Cable ta ruwaito.

Hakan na cikin wata sanarwar ne da mai magana da yawun yan sandan jihar Nasarawa, Rahman Nansel, ya fitar a ranar Laraba a Lafia.

Kara karanta wannan

Babu shakka sai mun binciko wadanda suka kashe dakarunmu, Hedkwatar tsaro ta fusata

The Cable ta ruwaito cewa Nansel ya ce kimanin yan bindiga biyar ne suka kutsa gidan sakataren na NASIEC a ƙauyen Bakin Rijiya da ke hanyar Lafia-Shendam misalin ƙarfe 11.45 na daren Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164