Babu shakka sai mun binciko wadanda suka kashe dakarunmu, Hedkwatar tsaro ta fusata

Babu shakka sai mun binciko wadanda suka kashe dakarunmu, Hedkwatar tsaro ta fusata

  • A ranar Talata hedkwatar tsaro ta lashi takobin bin sawun ‘yan bindigan da suka shiga har NDA suka ci karensu babu babbaka
  • Rahotanni sun bayyana kan yadda suka afka barikin Afaka dake NDA da misalin 1am suka kashe sojoji biyu kuma suka yi garkuwa da wani
  • A wata takarda da darektan labaran soji ya saki, ya ce Janar Lucky Irabor ya ce yanzu haka an dage wurin ganin an bincike ko ina don ceto sojan da suka sata

FCT, Abuja - A ranar Talata ne hedkwatar tsaro ta lashi takobin bin sawun ‘yan bindigan da suka shiga har barikin soji ta NDA suka ragargaji sojoji kuma suka yi garkuwa da wani.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an samu rahotanni akan yadda ‘yan bindiga suka afka har cikin barikin Afaka dake NDA, Kaduna inda suka kashe manyan sojoji biyu. Basu tsaya a nan ba har sai da suka yi garkuwa da wani babban sojan.

Kara karanta wannan

Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara

Babu shakka sai mun binciko wadanda suka kashe dakarunmu, Hedkwatar tsaro ta fusata
Babu shakka sai mun binciko wadanda suka kashe dakarunmu, Hedkwatar tsaro ta fusata. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sakamakon faruwar lamarin ne shugaban hukumar sojin kasa, Janar Lucky Irabor ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan inda yace yanzu haka an nunka tsaro a wuraren da lamarin ya faru.

Hedkwatar tsaro ta fitar da takarda

A wata takarda wacce darektan yada labaran soji, manjo janar Benjamin Sawyer ya saki a maimakon Irabor, ya ce an dage wurin bin duk wasu hanyoyin ganin an bi sawun miyagun mutanen don ceto sojojin da suka sata.

Yanzu haka jaruman sojin AFN sun fita don ganin sun riski ‘yan bindigan da suka shiga har dakunan sojoji a NDA dake Kaduna da safiyar 24 ga watan Augusta.
Yan bindigan sun lallaba ne da asuban fari ta katanga har dakunan sojojin inda suka bude wuta. Sai dai sun yi ajalin manyan sojoji biyu sannan sun yi garkuwa da daya.

Kara karanta wannan

Da wanne ido zaku kallemu, kun ji kunya sosai, 'Yan Najeriya sun caccaki hukumomin NDA

Yanzu haka ana iyakar kokarin ganin an ninka tsaro sannan ana bincike ko ina a wurin da lamarin ya faru don ceto sojojin da suka sace.
Yanzu haka shugaban NDA tare da HQ 1 Division tare da kokarin NAF sun hade kawunansu wurin nemo sojan da suka sace sannan su damki wadanda suka yi wannan aika-aika.
CDS yana so yayi amfani da wannan damar wurin yin ta’aziyya ga iyalan wadanda suka hallaka sannan yana godiya ga rundunar kan fara kokari cikin gaggawa.
CDS yana son tabbatar wa da mazauna yankin NDA cewa yanzu haka an nunka tsaro don tabbatar da lafiyarsu kuma ana cigaba da binciken yankin. Za a sake sakin wasu bayanai idan akwai bukatar hakan,” kamar yadda takardar tazo.

Sunayen hafsoshin soji 2 da 'yan bindiga suka sheke a NDA Kaduna

A wani labari na daban, a ranar Talata da sassafe ne wasu 'yan bindiga suka kai farmaki barikin Afaka dake NDA inda suka harbe wani soja mai mukamin Lieutenant Commander mai suna Wulah, da wani Flying Lieutenant CM Okoronwo har lahira.

Kara karanta wannan

Sunayen hafsoshin soji 2 da 'yan bindiga suka sheke a NDA Kaduna

Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan bindigan suka afka barikin da misalin karfe 1am.

Wata majiya daga barikin tace ana zargin wadanda suka kai farmakin sun bari ne daidai lokacin da mutane da dama suke bacci.

Asali: Legit.ng

Tags:
NDA
Online view pixel