Gidan Soja: Dalilin da yasa muke karbar tuban mayakan Boko Haram da suka mika wuya
- Rohoto daga rundunar sojin Najeriya ya bayyana dalilin da yasa sojoji ba sa kashe tubabbun 'yan Boko Haram
- A cewar wani jami'i yayin hira da gidan jarida, ya ce sojoji ba su da ikon daukar doka a hannunsu
- Ya kuma bayyana cewa, a matsayin su na kwararrun sojoji, abin kunya ne su ke daukar doka a hannu
Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa Sojojin Najeriya sun yi bayanin cewa babbar yarjejeniya ta duniya wanda Najeriya ta sanya hannu a kansa bai yarda a kashe 'yan ta'adda da suka mika wuya ba.
Leadership ta ruwaito cewa kakakin rundunar, Brig-Gen Onyema Nwachukwu ne, ya bayyana haka a wata hira.
Ya sake nanata cewa sojojin da aka tura don “Operation Hadin Kai” sun karbi ‘yan ta’addan Boko Haram/ ISWAP da suka mika wuya bisa ga dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar rikicin makamai.
Legit.ng ta lura cewa an bayar da bayanin ne yayin kiraye-kirayen da ake yi kan sojoji da su kashe 'yan ta'addan da suka mika wuya maimakon mayar da su cikin al'umma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An tattaro cewa sama da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP 3,000 ko dai aka kama su ko kuma suka mika wuya ga sojoji a arewa maso gabas a cikin watanni uku da suka gabata.
Me yasa 'yan ta'adda ke mika wuya?
Nwachukwu ya kuma ce guguwar mika kai da aka shaida ta kasance ne saboda hadewar dabaru don magance lamarin da ke haifar da kashe-kashe a yankin.
Ya bayyana cewa masu tayar da kayar bayar sun yanke shawarar yin watsi da manufarsu da gwagwarmayarsu ne bayan sun fahimci cewa gwagwarmaya ce ta banza.
Ya ce manyan kwamandojin kungiyar ISWAP sun hallaka kwamandojin Boko Haram cikin tsari yayin da aka yi watsi da sojojinsu na kasa.
Wannan, a cewarsa, shine dalilin da ya sa yan ta’addan Boko Haram ke mika wuya maimakon jerawa da ISWAP don biyan bukatun wasu mazauna kasashen waje masu son rusa Najeriya.
Nwachukwu ya kara da cewa:
“A matsayinmu na kwararrun sojoji, aikinmu shi ne mu tsare su, mu bayyana su sannan mu mika su ga hukumomin da abin ya shafa don ci gaba da daukar mataki.”
Soja ba shi da ikon gurfanar da 'yan ta'adda
Hakazalika cikin hirar, Kakakin rundunar sojin Najeriya ya ce sojoji ba su da ikon gurfanar da 'yan ta'adda yayin da aka kama su a yaki ko kuma suka mika wuya cikin sauki.
Yace:
“Ba ya daga cikin aikin sojoji gurfanar da su ko kuma sakin su. Hakanan zai zama rashin adalci ne a auna kowane matakin hukunci a namu bangaren. Ba za mu iya zama kwararrun sojoji ba mu dauki doka a hannunmu ba.
“Bai kamata a fassara wannan a matsayin sasantawa ko rauni ba. Maimakon haka, ya kamata a ga hakan a matsayin bin dokokin rikice-rikice na duniya da samar da tsarin mulkin Najeriya.”
Ya kuma fayyace cewa, maharan da suka mika wuya ba sa zaune a sansanin 'yan gudun hijira.
Karin 'yan Boko Haram sun mika kansu ga sojoji, suna rokon gafaran 'yan Najeriya
A wani labarin daban, Rahoto daga Daily Trust na shaida cewa, wasu mayakan Boko Haram sun mika wuya ga dakarun sojojin Najeriya.
A cewar majiyoyin soji, ‘yan ta’adda 190 sun mika wuya a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno a ranar Asabar.
An tattaro cewa mazauna garin sun yi mamaki lokacin da suka ga dimbin 'yan ta'addan da suka isa garin Mafa a ranar Asabar. A cewar majiyar tsaro, wadanda suka mika wuya sun hada da manyan mayaka, sojojin kafa, matansu da yaransu.
Rundunar sojin Najeriya ta yi martani yayin da matar marigayin kanal ta yi ikirarin cewa kashe mijinta aka yi
Asali: Legit.ng