Abubuwa 6 da ya kamata ka sani game da harin da yan bindiga suka kai NDA

Abubuwa 6 da ya kamata ka sani game da harin da yan bindiga suka kai NDA

Wasu tsagerun yan bindiga sun kai mumunan hari makarantar horar da Sojin Najeriya NDA dake jihar Kaduna.

Rahoton ya nuna cewa yan bindigan sun hallaka mutum biyu yayinda suka yi awon gaba da jami'in Soja guda daya.

An tattaro cewa yan bindigan sun kai farmakin ne misalin karfe 1 na dare.

Ga abubuwa 5 da ya kamata ku sani:

1. Yan bindigan sun samu shiga makarantar ne ta katanga kuma suka tafi rukunin gidaje kai tsaye suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

2. Sun yi awon gaba da Soja mai suna Manjo Datong.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Sun kashe Hafsoshi biyu; Laftanal Cadre Wulah da Flt Lt CM Okoronwo

Kara karanta wannan

Yan bindigan da suka kai hari NDA sun bukaci N200m kudin fansa

4. Wani Soja mai suna Lt Onah ya jikkata kuma yana jinya a asibiti

5. Yan bindigan sun kira, sunce suna bukatar N200m kudin fansa

6. Sojojin Najeriya sun lashi takobin nemo wadannan yan bindiga tare da ceto Sojan

Abubuwa 6 da ya kamata ka sani game da harin da yan bindiga suka kai NDA
Abubuwa 6 da ya kamata ka sani game da harin da yan bindiga suka kai NDA
Asali: UGC

NDA ta tabbatar da harin da aka kai mata, ta sha alwashin bin sawun 'yan ta'adda

NDA ta tabbatar da kisan jami’ai biyu a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari barikin a ranar Talata, 24 ga watan Agusta.

Sanarwar da jami'in hulda da jama'a na makarantar, Manjo Bashir Jajira ya fitar, ya ce 'yan bindigar sun sace wani jami'i.

NDA ta bayyana cewa tana kan bin diddigin 'yan fashin da suka yi kutse a tsarin tsaronta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng