Na Samar da Isasshen Fasahar Zamani da Za'a Magance Matsalar Tsaro, Sheikh Pantami
- Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, yace ya samar da fasahar da za'a magance tsaro
- Ministan yace duk abinda hukumomin tsaro suka bukata daga ɓangarensa yana samar musu ɗari bisa ɗari
- A cewarsa sauran aikin ya rage nasu, yin amfani da abubuwan da aka samar musu yadda ya kamata
Abuja - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dakta Isa Pantami, yace ya yi bakin kokarinsa wajen samar da isashen fasahar zamani da zai taimaka wa hukumomin tsaro su magance matsalar tsaro a faɗin kasar nan.
Pantami ya faɗi haka ne a Abuja, ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai, jim kaɗan bayan an gabatar masa da wani littafi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
A jawabinsa, Pantami yace:
"Amfani da fasahar zamani yana taka rawar gani wajen magance matsalar tsrao, amma a ɓangaren mu, ba mune hukumomin tsaron kasar nan ba."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mun samar wa jami'an tsaro komai da suka bukata
Malam Pantami yace tun bayan da ya karbi ragamar ma'aikatar sadarwa yake taimaka wa hukumomin tsaro.
Pantami yace:
"Tun bayan da na shiga ofis ɗin minista nake taimakawa hukumomin tsaro. Duk wani taimako da suke bukata na fasaha da zai taimaka musu a aikinsu, ina samar musu 100%."
"Sauran ya rage gare su yin amfani da fasahar da muka samar, domin ba aikin mu bane, mu fada musu abinda zasu yi. Duk abinda suka bukata mun samar musu 100% kuma zamu cigaba da haka."
Yaushe za'a saka 5G a Najeriya?
Dangane da 5G kuwa, Pantami yace an kammala dukkan shirye-shirye kuma za'a gabatar da kunshin ga majalisar zartarwa, bayan kwamitin da aka kafa sun kammala aikinsu.
Yace gwamnati ta fara shirin sanya 5G tun shekarar da ta gabata 2020, amma sai annobar korona ta dakatar da komai.
A wani labarin kuma Babban Malami Ya Bayyana Yankin da Ya Dace Ya Fitar da Wanda Zai Gaji Buhari a 2023
Shugaban coci-cocin Citadel Global Community, Fasto Tunde Bakare , yace arewa zata iya samar da shugaban ƙasan da zai gaji Buhari, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Bakare ya kara da cewa kowace jam'iyya ta yi iyakar bakin kokarinta wajen fitar da ɗan takara sauran kuma abarwa masu kaɗa kuri'a su tantance.
Asali: Legit.ng