'Yan bindiga sun datse hanyoyin samar da fetur ga yankunan Zamfara bayan sun bankawa tanka wuta

'Yan bindiga sun datse hanyoyin samar da fetur ga yankunan Zamfara bayan sun bankawa tanka wuta

  • ‘Yan bindiga sun dakatar da shigar da man fetur a garin Dansadau da sauran makwabtansu tun bayan banka wa tankar mai wuta da suka yi a hanyar Gusau zuwa Dansadau
  • Tankar man tana daya daga cikin ababen hawan da jami’an tsaro suka raka zuwa Dansadau a ranar Talata, daga nan ne ‘yan bindigan suka bude mata wuta
  • Mai tankar, Alhaji Yau Muhammad Dansadau ya shaida wa manema labarai cewa tun daga gidan man NNPC dake Gusau tankar ta taho don kai mai garin

Zamfara - Wasu ‘yan bindiga sun dakatar da shigar da man fetur garin Dansadau da makwabtansa tun bayan banka wa wata tankar mai da ta taho daga Gusau zuwa Dansadau wuta.

Daily Trust ta ruwaito cewa, tankar daya ce daga cikin sauran ababen hawan da jami’an tsaro dauke da makamai suka raka garin Dansadau a ranar Talata, kwatsam kuma sai ‘yan bindigan suka bude mata wuta.

Kara karanta wannan

Harin Kwalejin sojoji ta Najeriya: Dalilai 3 da suka sa ‘yan ta’adda samun nasara

'Yan bindiga sun datse hanyoyin samar da fetur ga yankunan Zamfara bayan sun bankawa tanka wuta
'Yan bindiga sun datse hanyoyin samar da fetur ga yankunan Zamfara bayan sun bankawa tanka wuta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mai tankar, Alhaji Yau Muhammad Dansadau ya bayyana wa Daily Trust cewa, tun daga gidan man NNPC dake Gusau tankar take don samar da man fetur a garin sakamakon rashin mai wanda ya janyo aka rufe gidajen mayuka da dama.

Har yanzu ba a san inda direban tankar da wani da suke tare suke ba. Wata kila an yi garkuwa dasu. Sai dai babban abin tsoron shine yadda za a fara fama da rashin mai a garin nan ba da dadewa ba. Motoci da sauran ababen hawa da suke amfani da fetur za su daina aiki,” a cewarsa.
An fada min cewa ba tankar man kadai suka kai wa farmaki ba, har da wasu ababen hawan. Hakan ya sanya mutane suka dinga tserewa don neman tsira duk da dai sun yi bata-kashi da ‘yan sandan da suka rako tankar.

Kara karanta wannan

Jama’a sun ji hudubar Gwamnoni, sun tanadi bindigogi saboda gudun bacin rana

Yanzu haka babu abin hawan da zai iya bin titi matsawar babu jami’in tsaron da zai raka shi. Don sun kashe mutane da dama musamman ‘yan kasuwa da direbobin motar haya, sannan sun yi garkuwa da wasu a titin nan mai tsawon 100km abin ya fi tsananta.
Farmakin ya fi aukuwa a daidai Mashayar Zaki, wanda tafiya kadan ne mutum zai yi ya isa Dansadau. ‘Yan bindigan suna labe suna jiran su ga wani abin hawa don su kai farmaki,” a cewar Ya'u.

‘Yan bindiga sun rantse akan sai sun dakatar da shigar duk wasu kayan masarufi zuwa garin Dansadau tun bayan da aka rufe kasuwanni kuma aka dakatar da duk wata hanya da za su dinga samun abinci, ababen sha da kayan amfani a dazukan da suke zama.

Jami'an MNJTF sun sheke 'yan ta'adda 4, sun kwace miyagun makamai a Borno

A wani labari na daban, jami’an MNJTF sun ragargaji ‘yan bindiga 4 a wani karon batta da suka yi wuraren tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Kuma dai: An kashe dalibin jami’ar Jos ‘yan awanni bayan Lalong ya saukaka dokar kulle

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wata takarda wacce Kanal Muhammad Dole, shugaban fannin watsa labaran MNJTF, ya fitar a ranar Litinin a Maiduguri jihar Borno, ta ce sun samu nasarar kwato miyagun makamai daga hannun ‘yan ta'addan.

Sakamakon kara kaimi da sojoji suka yi sun samu nasarar ragargaje mayakan Boko Haram da na ISWAP wuraren tafkin Chadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel