Jami'an MNJTF sun sheke 'yan ta'adda 4, sun kwace miyagun makamai a Borno

Jami'an MNJTF sun sheke 'yan ta'adda 4, sun kwace miyagun makamai a Borno

  • Jami’an MNJTF sun halaka ‘yan bindiga hudu a wani karon batta da suka yi a wuraren tafkin Chadi
  • Sun bayyana hakan ne a wata takarda wacce shugaban fannin watsa labaran MNJTF ya saki a ranar Litinin
  • Kamar yadda ya tabbatar, mayakan Boko Haram da na ISWAP din ne suka kai musu hari a wuraren Gajiram

Borno - Jami’an MNJTF sun ragargaji ‘yan bindiga 4 a wani karon batta da suka yi wuraren tafkin Chadi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wata takarda wacce Kanal Muhammad Dole, shugaban fannin watsa labaran MNJTF, ya fitar a ranar Litinin a Maiduguri jihar Borno, ta ce sun samu nasarar kwato miyagun makamai daga hannun ‘yan ta'addan.

Jami'an MNJTF sun sheke 'yan ta'adda 4, sun kwace miyagun makamai a Borno
Jami'an MNJTF sun sheke 'yan ta'adda 4, sun kwace miyagun makamai a Borno. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Abinda takardar ta kunsa

Sakamakon kara kaimi da sojoji suka yi sun samu nasarar ragargaje mayakan Boko Haram da na ISWAP wuraren tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Wadanda suka halarci walimar Yusuf Buhari da Zahra Bayero sun samu Iphone 12 Pro, Ipad

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rundunar MNJTF yanki na uku na Monguno sun yi zagaye wuraren Gajiram, kwatsam suka gamu da mayakan Boko Haram da na ISWAP sun kai hari wuraren Gambari.
Sojoji sun samu nasara a karon battan inda suka ragargaje ‘yan ta’adda hudu wadanda suka ce ga garinku take yanke, yayin da wasu da dama suka tsere da miyagun raunuka.
Sai dai daya daga cikin sojojin ya samu rauni kuma yana asibitin soji ana kulawa da lafiyarsa,” Kamar yadda Dole yace.

Ya ce an samu bindigogi kirar AK 47 guda 3, special rounds na 7.62 guda 10 da miyagun kwayoyi da sauransu, Daily Trust ta ruwaito.

Manjo janar Abdul Khalifah, wanda shi ne sabon kwamandan MNJTF wacce hedkwatarta take a Ndjamena a Chadi ya samu damar kai ziyara ga sojoji na wurare daban-daban inda ya kara musu kaimi kuma ya bukaci su kara dagewa wurin kawar da ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Sojojin hadaka sun ragargaji 'yan Boko Haram da ISWAP a Borno, sun hallaka wasu adadi

Malami, Dingyadi, da sauran jiga-jigan da suka halarci auren 'ya'ya 10 na Wamakko

A wani labari na daban, ministan kula da harkokin 'yan sanda, Muhammadu Maigari Dingyadi, Ministan shari'a, Abubakar Malami da gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, suna daga cikin jiga-jigan da suka halarci bikin auren 'ya'ya 10 na Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a ranar Lahadi.

Daily Trust ta tattaro cewa ministocin sun wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a wurin bikin.

Sauran jiga-jigan da suka halarci bikin sun hada da tsoffin Gwamnonin Sokoto da Zamfara, Yahaya Abdulkareem da Abdulazeez Yari, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Yahya Abdullahi wanda ya wakilci shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawal da sauran 'yan majalisu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel