Jama’a sun ji hudubar Gwamnoni, sun tanadi bindigogi saboda gudun bacin rana
- Mutane suna mallakar makamai domin su kare kansu daga harin ‘Yan bindiga
- Wasu sun saye bindiga ba tare da sun samu iznin mallaka ko lasisin hukuma ba
- Al’umma sun koma wa rike makamai ne saboda jami’an tsaro sun gaza tsare su
Daily Trust ta ce Al’umma suna sayen bindigogi da sauran makamai da nufin kare kansu daga ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda a wasu jihohin da ke Najeriya.
Binciken da jaridar ta yi ya nuna cewa masu hali suna mallakar manyan bindigogi ko kuma su saya wa kungiyoyin ‘yan sa-kai saboda a tsare rai da dukiyar jama’a.
A ina lamarin ya fi auku wa?
Kauyukan Neja, Zamfara, Kaduna, Filato da Katsina suna cikin inda aka fi fama da matsalar tsaro a yau.
Mazauna kauyukan wadannan yanki sun shaida wa jaridar cewa sun nemi hanyoyin da za su kare kansu da kansu domin jami’an tsaro sun gagara tsare jininsu.
Abin da mazauna da shugabannin al’umma a kauyukan suka fada ya zo daidai da kiran da wasu gwamnnoni suke yi na cewa kowa ya tanadi makamin da zai rike.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton yace mazauna na sayen bindigar katako, harba-ka-labe, kananan bindigogi da AK-47. Ana yawan mallakar makaman ba tare da hukuma ta bada lasisi ba.
A yankin Shiroro, mutanen gari sun tanadi kananan bindigogi da ake hada wa a gida da nufin kare kansu duk lokacin da ‘yan bindiga suka kawo harin da suka saba.
Duk da gwamnati ba ta yarda da hakan ba, wani mazaunin karamar hukumar Rafi ya bayyana cewa kwanaki suka kashe ‘yan bindiga goma da suka kawo masu hari.
A yankunan Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun a Kaduna, akwai mutanen da suka hakura da neman agaji daga jami’an tsaro, sun dauki matakin kare rayuwarsu.
Wani mazaunin garin Giwa ya bayyana cewa sun dade da sanin gwamnati ba za ta iya kare su ba, don haka ne suka tanadi makamansu ba ko tare da iznin hukuma ba.
A Filato da Zamfara haka abin yake, mutane suna zuwa wurin makera su hada masu bindiga, wasu kan bi hanyar da ta dace domin su samu lasisin ajiye makami.
Akwai tsaro a Kogi
Magoya bayan Gwamna Yahaya Bello sun jefa wa Kungiyar Bola Tinubu martani. ‘Yan GYB2PYB sun ce an daina yayin tsofaffin shugabanni yanzu a kasashen Duniya.
Kungiyar Governor Yahaya Bello to President Yahaya Bello ta ce gwamnan ya yi kokarin wajen kawo tsaro da zaman lafiya a Kogi, har Amurka ta tabbatar da wannan.
Asali: Legit.ng