Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Tsige Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa Secondus

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Tsige Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa Secondus

  • Rikicin cikin gida a babbar jam'iyyar hamayya PDP ya sake bude sabon shafi kan shugabanci
  • Wata babbar kotu dake zamanta a jihar Ribas ta dakatar da Uche Secondus daga natsayin shugaban PDP na kasa
  • Kotun ta bada umarnin hana Secondus shiga dukkan al'amuran jam'iyyar PDP a kowane mataki

Rivers - Rikicin babbar jam'iyyar hamayya PDP ya sake ɗaukar wani sabon salo ranar Litinin a jihar Ribas, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Wata babbar kotu a jihar Ribas ta dakatar da Uche Secondus daga bayyana kansa a matsayin shugaban PDP na kasa.

Secondus, wanda yake ta faɗi tashin rike mukaminsa, an ba shi damar ya shirya gangamin taron jam'iyyar a watan Oktoba.

Shugaban PDP, Uche Secondus
Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Tsige Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa Secondus Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta gano cewa Secondus ya matsa cewa dole a barshi ya karisa wa'adin mulkinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotu ta dakatar da Secondus daga ɗaukar kansa Shugaba

Mai shari'a O. Gbasam, ya tumɓuke Uche Secondus daga matsayin shugaban PDP yayin da yake yanke hukunci kan karar da jiga-jigan PDP suka shigar akansa.

Waɗanda suka shigar da karar sun haɗa da, Ibeawuchi Ernest Alex, Dennis Nna Amadi, Emmanuel Stephen da kuma Umezirike Onucha.

Alkalin kotun ya kuma hana Secondus jagorantar shirya gangamin taron PDP na gundumomi da da kananan hukumomi, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Wani sashin jawabin Alkalin yace:

"Kotu da bada umarnin hana wanda ake kara daga bayyana kanshi a matsayin shugaba ko kuma gudanar da ayyukan shugaba."
"Hakanan kotu ta umarci hana wanda ake kara kira, halarta ko jagorantar wani taro ko shiga wani kwamiti a matakin gunduuma, karamar hukuma ko jiha.
"Kuma an hana wanda ake kara daga shirya gangamin taron gundumomi, kananan hukumomi ko jiha yayin da aka dakatar da shi daga kasancewa ɗan jam'iyya."

A wani labarin kuma Wajibi Gwamnatin Shugaba Buhari Ta Rage Ciyo Bashi, Sanata Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, yace ya zama wajibi a nemo hanyar rage ciyo bashin gwamnatin tarayya.

Lawan ya bayyana haka ne jin kaɗan bayan fitowa daga wata ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel