Ba'a Taba Shugaban Ƙasa da Ya Lalata Harkar Tsaro ba Kamar Buhari, Gwamna
- Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, yace ba'a taba yin gwamnati mai muni kamar ta Buhari ba a bangaren tsaro
- Gwamnan yace shugaba Buhari ya ki maida hankali tare da baiwa ɓangaren muhimmancin da ya kamata
- Ortom yace Buhari ya kawo cigaba a wasu ɓangarori amma ɓangaren tsaro sai abinda ya kara muni
Abuja - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari, inda ya bayyana ta mafi muni a ɓangaren tsaron ƙasa.
Gwamnan wanda ya bakunci shirin Channels tv na Sunrise Daily ranar Talata, yace baya jin dadin yadda Buhari yake rikon sakainar kashi da muhimman lamurra musamman tsaro.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne yayin da yake martani kan matakin da shugaba Buhari ya ɗauka kan kiwon fili.
Ina tunanin ko yana da boyayyar manufa?
Gwamna Ortom yace:
"Shugabana ƙasa yana tilasta mun tunani kan abinda wasu mutane ke faɗa akansa, cewa ko dai yana da wata manufa a ƙasar nan gaskiya ne."
"Saboda abun ya fito fili cewa Buhari yana son maida kasar nan ta Fulani kuma ba shine bafullatanin shugaban ƙasa na farko ba."
"Shagari bafullatani ne, haka ma Yar'adua kuma sune shugabanni nagari da ake tunawa a tarihi. Amma shugaba Buhari shine shugaba mafi muni a ɓangaren tsaro da kuma cika alkawari."
Buhari ba shi da cika alkawari
Ortom ya bayyana cewa idan ka koma baya shekarar 2015, babu alkawarin da Buhari ya cika daga cikin waɗanda ya ɗauka.
"Idan kaduba maganganun da yayi a 2015 game da yancin ɗan adam, yancin magana, tattalin arziki, tsaro, cin hanci da rashawa, ku faɗamun wanne ya cika a ciki?"
"Ya cimma nasara wajen kawo cigaba a wasu ɓangarori amma waɗannan muhimman bangarorin da suka addabi yan Najeriya, ku faɗa mun wanne shugaban kasa yake kokarin magance wa?"
"Yaki da cin hanci ne kaɗai kuma shima ya zama mafi muni a tarihin wannan ƙasar."
A wani labarin kuma Ba Gudu Ba Ja da Baya, Kungiyar Likitoci NARD Ta Maida Martani Kan Umarnin Kotu
Kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD) ta maida martani kan hukuncin kotun ma'aikata "mai rikitarwa" na ranar Litinin, inda tace sam bata san da zaman kotun ba.
Legit.ng Hausa ta ruwaito muku cewa kotun dake zamanta a Abuja ta umarci ɓangarori biyu, gwamnati da NARD, su jingine duk wani rashin jituwa su rungumi sulhu.
Asali: Legit.ng