'Yar musulma ta samu tallafin fasto, mahaifiyarta ta durkusa a coci domin nuna godiya
- Wata shahararriyar Fasto ta tallafawa wata 'yar shekaru 12 musulma da gurbin karatu na makudan kudade
- Mun tattaro cewa, an ga fasto din da mahaifiyar yarinyar suna zubar kwalla yayin da mahaifiyar ke godiya a coci
- Mutane da dama sun yi martani kan wannan lamari, in da suka bayyana ra'ayoyinsu kan wannan aiki
Shahararriyar malamar addinin kirista Fasto Rose Kelvin, wadda ta kafa cocin Prophetess Rose Kelvin Ministry, ta bai wa wata yarinya Musulma 'yar shekara 12 mai suna Latifat tallafin karatu.
Da ake ba da labarin yadda lamarin ya kasance, Fasto Rose Kellvin, wacce aka fi sani da Mummy Rose an ce tana neman mai aikin gida ne lokacin da ta hadu da yarinyar.
Lokacin da ta ga matashiyar cewa za ta iya yi mata aikin gida, Rose ta tambayi halin da take ciki kuma ta fahimci cewa Latifat ta bar zuwa makaranta saboda matsalar kudi.
Latifat, haifaffiyar iyalin da ke da mutum 5, ta koma sana'ar aikatau don taimakawa mahaifiyarta da ke rokon sadaka bayan da mijinta ya bar su shekaru biyu da suka gabata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Fasto Rose ta bai wa Latifat tallafin karatu da ya kai zunzurutun kudi N300,000 don taimakawa yarinyar ta kammala karatun sakandare.
A cikin hotunan da muka samo an yada a shafin Facebook na fasto din, Misis Hawau, mahaifiyar Latifat ta durkusa cikin hawaye a cikin coci don godiya ga malamar bisa namijin kokari da ta yi na tallafawa 'yar ta.
An ga Fasto Rose sheshsheka a hankali yayin da ta rungumi mahaifiyar Musulma mai cike da hawaye da 'yar ta.
Kalli hotunan:
Mutane a kafar Facebook sun yi martani kan lamarin
Chinagorom Onuigbo ya rubuta:
"Wannan baiwar Allah ce!! Wannan shine abin da nake rokon Allah da ya ba ni irin wannan zuciya!! Rayuwa ba tare da bayarwa ba ita ce cin mutuncin mahaliccinmu domin mun shigo duniya ba tare da komai ba kuma za mu koma da komai ba!! ! Allah ya albarkaci rayuwar mummy Rose."
Ukamaka Gloria ta rubuta:
"Chaii mace mai mutunci, bakin salama na Allah, uwa ga mara uwa, da fatan Allah ya ci gaba da daga ki sama, mafi alheri..."
Titilayo Nobore yayi sharhi:
"Mummy godiya da taimakon dangin da ke cikin bukata a ko yaushe kina kasancewa babbar alfarma ga mutane godiya da jinjina mafi alheri, ina kaunarki."
Obinna Onunkwo ya ce:
"Mummy abin da kike yi yana da kyau amma don Allah kiyi tunanin gida, ina rokon ubangiji mai zai taimaka ki fahimci wannan sakon. Ki taimaka wa 'yan uwanmu igbo don su taimaka mana. Gabashin yamma arewa da kudu gida shine mafi kyau a yanzu."
Farfesa Aminu Dorayi: Bakanon da ya tuko motarsa daga Landan har zuwa Kano
A wani labarin, Farfesa Aminu Mohammed Dorayi ba kawai cikakken dan boko bane mai zurfin karatu kuma dattijon kasa, idan ana maganar tarihi, ya kafa tarihi mai kyau da ban al'ajabi a rayuwarsa wanda ba za a iya mantawa ba.
Abusites sun ruwaito cewa Farfesa Aminu wanda ya taba kasancewa Shugaban Gwamnatin Kungiyar Dalibai na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya taba wata tafiya daga birnin London har zuwa babban birnin Kano shekaru da yawa da suka gabata da motarsa.
Farfesan dan asalin jihar Kano, a cikin wata hira da Daily Trust a 2019 ya ba da labarin yadda ya yi tafiyar wacce ta dauke shi kwanaki 24 a cikin motarsa kirar Peugeot 504.
Asali: Legit.ng