2023: Hadimin Osinbajo ya bayyana ra'ayin ubangidansa kan tsayawa takarar shugabancin kasa

2023: Hadimin Osinbajo ya bayyana ra'ayin ubangidansa kan tsayawa takarar shugabancin kasa

  • Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya musanta rade-radin dake yawo na cewa zai fito takarar shugabancin kasa
  • Kamar yadda hadiminsa, Laolu Akande ya bayyana, ya ce wannan hanya ce ta daukewa ubangidansa hankali kawai
  • Ya sanar da cewa ya mayar da hankali wurin shawo kan matsalolin Najeriya a fannin tsaro da tattalin arziki

FCT, Abuja - Laolu Akande, mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya ce ubangidansa bai bayyana burinsa na takarar shugabancin kasa ba, akasin yadda ake ta yadawa a kafafen sada zumunta.

A wata takarda da Akande ya fitar a ranar Litinin, ya ce mataimakin shugaban kasan ya mayar da hankali ne wurin aiki kan matsalolin da kasar nan ke fama da su.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke 'yar leken asirin 'yan IPOB masu kone-konen kayan gwamnati

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya kwatanta rahotannin da hanyoyin dauke masa hankali inda ya shawarci masu wannan wallafar da su daina.

2023: Hadimin Osinbajo ya bayyana ra'ayin ubangidansa kan tsayawa takarar shugabancin kasa
2023: Hadimin Osinbajo ya bayyana ra'ayin ubangidansa kan tsayawa takarar shugabancin kasa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
An sake samun wasu irin al'amura kamar sakin salon yakin neman zabe, bidiyoyi, fastoci a kafafen sada zumunta da kuma wadanda aka manna a wasu sassan kasar nan da suka hada da babban birnin tarayya da Kano, inda ake cewa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya shiga takarar neman kujerar shugabancin kasa.
Ofishin mataimakin shugaban kasa ya janye kansa daga makamancin wannan al'amarin a watan Mayun wannan shekarar. Ofishin mataimakin shugaban kasan bashi da alaka da wannan al'amari.
Wadannan kananan abubuwa ne da aka kirkiro domin janye hankalinsa daga ayyukan gwamnati a kasar nan.
Farfesa Osinbajo bai nuna muradinsa na fitowa takara ba a 2023, amma ya mayar da hankali wurin aiki a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa wurin shawo kan matsalolin kasar nan da kuma damuwar 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin yan bindiga a Kaduna kan raba kudin fansa, sun kashe juna har mutum 9

Hakan ya hada da shawo kan matsalolin tsaron da suka yi katutu a kasar nan da kuma nemo hanyoyin inganta tattalin arzikin kasar nan.
A don haka ana shawartar jama'a da su daina wannan wallafar a yayin da muke mayar da hankali wurin shawo kan matsalar Najeriya domin ta koma kasa mai cike da zaman lafiya da arziki," takardar tace.

Malami, Dingyadi, da sauran jiga-jigan da suka halarci auren 'ya'ya 10 na Wamakko

A wani labari na daban, ministan kula da harkokin 'yan sanda, Muhammadu Maigari Dingyadi, Ministan shari'a, Abubakar Malami da gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, suna daga cikin jiga-jigan da suka halarci bikin auren 'ya'ya 10 na Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a ranar Lahadi.

Daily Trust ta tattaro cewa ministocin sun wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a wurin bikin.

Sauran jiga-jigan da suka halarci bikin sun hada da tsoffin Gwamnonin Sokoto da Zamfara, Yahaya Abdulkareem da Abdulazeez Yari, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Yahya Abdullahi wanda ya wakilci shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawal da sauran 'yan majalisu.

Kara karanta wannan

Tsabar Cin Bashi: Majalisar Wakilai ta yi wa Buhari Wankin Babban Bargo

Asali: Legit.ng

Online view pixel