Tsabar Cin Bashi: Majalisar Wakilai ta yi wa Buhari Wankin Babban Bargo

Tsabar Cin Bashi: Majalisar Wakilai ta yi wa Buhari Wankin Babban Bargo

  • Majalisar wakilai ta bayyana rashin amincewarta a kan yadda wasu bangarorin gwamnati suke adana kudaden shigarsu
  • Ta hassala akan yadda hakan ya janyo har sai gwamnatin tarayyar Najeriya ta rankaya kasashen ketare ta tattago bashi
  • Majalisar ta caccaki yadda gwamnatin ta yanke shawarar jajibar bashin naira tiriliyan 5.62 don cikasa kasafin shekarar 2022

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta nuna alhininta a kan yadda wasu bangarorin gwamnati suke adana kudin shigarsu da suke tarawa suna barin gwamnatin tarayya da nemo kudin kasafi.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda majalisar ta soki yadda gwamnati ta ketara kasar waje don cin bashin naira tiriliyan 5.62 don cikasa kasafin shekarar 2022, yayin da wadannan bangarorin gwamnatin suke killace kudaden a asusansu.

Kara karanta wannan

Hamshakin biloniya ya rasa diyarsa, watanni 2 bayan dan shi ya sheke kansa

Tsabar Cin Bashi: Majalisar Wakilai tayi wa Buhari Wankin Babban Bargo
Tsabar Cin Bashi: Majalisar Wakilai tayi wa Buhari Wankin Babban Bargo. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Facebook

Majalisar wakilai ta hassala da yadda ake aro kudade

James Faleke, shugaban kwamitin majalisar a fannin kudade ya bayyana hakan ne a wani taro na sauraron MTEF da FSP na shekarar 2022 zuwa 2024 a ranar Alhamis a Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba mu ji dadin yadda Najeriya take narkar bashin naira tiriliyan 5.62 ba kuma yanzu haka akwai kudade a kasa wadanda ba a riga an yi amfani dasu ba.
Tsakani da Allah ya kamata mu gina kasar nan tare ne saboda mu amfana,” a cewarsa.

Faleke yace babban matsalar da muke fuskanta a kasar nan shine samar da kudaden shiga, inda ya kara da cewa majalisar wakilai za ta fi son ta ji nawa ma’aikatu suke tarawa, Daily Nigerian ta ruwaito.

A cewarsa, matsawar majalisar wakilai ta gano cewa akwai wata ma’aikata ta gwamnati wacce ba dole bane aikinta, za a cire ta don sassautawa kasafin kasa.

Kara karanta wannan

A karon farko, tsohon Gwamna Dickson ya magantu kan tuhumarsa da EFCC take yi

Kwamitin ya bukaci NCC da ta samar da bayanin yawan kudaden da aka samu daga dukkan kamfanonin sadarwa tun daga 2018 zuwa 2020.

Gwamnatin Gombe Ta Kashe N100m a 2021 Kan Kiristoci Mahajjata, Jami'ai

A wani labari na daban, Karu Ishaya, sakataren hukumar samar wa da mahajjatan addinin kirista walwala, CPWB, na jihar Gombe ya bayyana yadda gwamnatin jihar Gombe ta kashe fiye da naira miliyan 100 wurin daukar nauyin mahajjatan kiristoci 70 zuwa kasar Jordan.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Ishaya ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Otal din Dead Sea Spa dake Sweimeh a Jordan yayin amsa tambayoyin manema labarai.

A cewarsa irin karamcin da gwamnatin jihar ta nunawa masu bautar ya sa su matukar farin ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel