Obasanjo ya yi addu'ar Allah ya ɗauki ransa: Na ga uku, bana addu'ar ganin Olu na Warri na huɗu

Obasanjo ya yi addu'ar Allah ya ɗauki ransa: Na ga uku, bana addu'ar ganin Olu na Warri na huɗu

  • Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Nigeria ya yi addu'ar kada Allah ya bashi tsawon ran ganin Olu na Warri na hudu
  • Tsohon shugaban kasar ya yi wannan addu'ar ne yayin da ya ziyarci sabon Olu na Warri na III, Ogiame Atuwatse III a Jihar Delta
  • Obasanjo ya bawa sabon sarkin shawarar ya kusanci Allah sannan ya dukufa wurin hada kan al'ummarsa da kawo cigaba

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta, a ranar Lahadi sun jagoranci manyan mutane da dama zuwa hallartar addu'ar ban godiya na nadin sarautar Mai Martaba Ogiame Atuwatse III, rahoton Arise News.

Da ya ke magana wurin taron, Obasanjo ya bukaci sabon sarkin na Itsekiri ya yi aiki domin hada kan masarautarsa da ma Nigeria baki daya.

Kara karanta wannan

Ba zai yiwu in bar mulki a kunyace ba: Shugaba Muhammadu Buhari

Obasanjo ya yi addu'ar Allah ya ɗauki ransa: Na ga uku, bana addu'ar ganin Olu na Warri na huɗu
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Olu na Warri na III, Ogiame Atuwatse III. Hoto: Ubi Franklin
Asali: Facebook

Ina addu'ar Allah yasa ba zan ga Olu na Warri na huda ba, Obasanjo

Tsohon shugaban kasar ya ce ya yi matukar sa'an ganin nadin sarautan Olu guda uku, yana mai cewa baya fata ko addu'ar ganin nadin wani Olun na Warri, Arise News ta ruwaito.

Ya yi wa sabon sarkin addu'a, yana mai cewa Allah ya ja zamaninsa cikin zaman lafiya, ya kuma bashi ikon hada kan al'umma da kawo cigaba a kasar Itsekiri.

Obasanjo ya ce:

"Ina daya daga cikin masu murna da nadin ka domin Allah ya bani baiwar ganin nadin Olu guda uku kuma bana addu'ar in ga na hudu.
"Ina son in jaddada cewa Allah ne ya baka wannan sarautar, amma tare da mutanen da ke kewaye da kai, dole ka rika tuna hakan.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo yayi magana akan ta’addancin da ke ta'azzara a Najeriya

"Idan Allah ya baka damar yi wa mutane hidima, rashin yin hakan saba wa Allah ne."

Tsohon shugaban kasar ya ce sarautar na tattare da nauyi, yana mai cewa sarkin ya fara da kyau kuma yana fatan zai jagoranci mutanen Itsekiri zuwa sabuwar alkarya.

Obasanjo ya ce:

"Ka kusanci Allah a duk abin da ka ke yi, tabbas Allah zai maka jagora."

Sauran manyan baki da suka hallarci taron?

Sauran manyan baki da suka hallarci addu'ar da aka yi a cocin fadar Olu na Warri sun hada da tsaffin gwamnonin Jihar Delta, Cif James Ibori da Dr Emmanuel Uduaghan, tsohon shugaban CAN, Ayo Oritsejafor da sauransu.

An nada Ogiame Atuwatse na III ne a matsayin Olu na Warri na III a ranar Asabar a Ose-Itsekiri, gidan gado na Itsekiri, a karamar hukumar Warri na Jihar Delta.

Wasu daga cikin manyan bakin sun yi jawabi inda suka yi wa sabon sarkin addu'a tare da bashi shawarwari.

Kara karanta wannan

Obasanjo: Kara yawa da al'ummar Afrika ke yi na hana ni bacci cikin dare

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164