FIRS na neman hanyoyin tatsar kudi, Twitter da sauran kamfanoni za su soma biyan haraji a 2022

FIRS na neman hanyoyin tatsar kudi, Twitter da sauran kamfanoni za su soma biyan haraji a 2022

  • Hukumar FIRS ta na sa rai ta karbi harajin Naira Tiriliyan 10 a shekara mai zuwa
  • Shugaban FIRS, Mohammed Nami ya bayyana wannan da ya ziyarci ‘Yan Majalisa
  • Nami yace irinsu Twitter za su fara biyan haraji, don haka kudin-shigan zai karu

Abuja - Hukumar FIRS mai tattara haraji a kasa ta ce ta ci burin samun Naira tiriliyan 10.1 a shekarar 2020, The Cable ta fitar da wannan rahoto.

Meya faru FIRS ta kara kudi?

Shugaban hukumar da ke da alhakin tattaraa harajin, Mohammed Nami, ya bayyana wannan a lokacin da ya bayyana gaban ‘yan majalisar wakilai.

Da yake jawabi a ranar Laraba, 18 ga watan Agusta, 2021, shugaban na FIRS yace kudin zai karu saboda kafofin sadarwan zamani za su fara bada haraji.

Ana sa ran a shekarar badi irinsu kamfanin Twitter za su rika biyan gwamati haraji, don haka kudin-shigan zai karu da har kusan Naira tiriliyan biyar.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya jagoranci zaman FEC na farko, ya amince a sayo karnukan N650m

Mohammed Nami yace idan an samu kudin, gwamnatin tarayya za ta tashi da Naira Tiriliyan 2.05, sauran za su tafi ga jihohi da kananan hukumomi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Jimillar abin da muke kokarin mu tattara, mu mika wa gwamnatin tarayya a asusunta, har da asusun hadaka a shekarar 2022 shi ne Naira tiriliyan 10.1.”
Shugaban FIRS
Shugaban FIRS na kasa, Mohammed Nami Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

An bada shawarar a sa wa Twitter haraji

“Game da kafofin tattalin arziki na zamani, mun dauki shawarar da ku ka bada, muna da sashen karbar harajin kamfanonin waje da zai yi aikin.”
“Twitter da sauransu sun fara yin rajista da mu, saboda haka muna sane. Muna sa rai za a ci moriyar wannan rajista da ake yi da hukumar FIRS.”

Da yake bayanin nasarorin da hukumar ta samu a karkashinsa, Nami ya ce a shekarar 2020, FIRS ta iya samun N4.950tr daga cikin N5.076tr da ta sa ran samu.

Kara karanta wannan

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

Bugu da kari, Premium Times ta rahoto Nami ya na cewa zai shigo da dabarun zamani na karbar haraji a tituna domin a fadada hanyoyin samun kudin-shiga.

APC ta sauke nauyin ta - Lawan

Shugaban majalisar dattawa na Najeriya, Ahmad Lawan ya yi kira ga gwamnatin APC ta cika alkwuran da ta daukarwa kan ta domin ta cigaba da mulki.

‘Dan siyasar ya kuma bada shawarar a rika tafiya da matasa idan ana son samun nasara a siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel