'Yan sanda da sojoji sun tsananta sintiri ta kasa da jiragen sama a Zamfara

'Yan sanda da sojoji sun tsananta sintiri ta kasa da jiragen sama a Zamfara

  • Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara da wasu hukumomin tsaro sun tsananta sintiri a Zamfara
  • An samu bayanai kan cewa miyagun 'yan bindiga za su kai farmaki wasu yankunan Tsafe na jihar
  • Jami'an tsaron sun bukaci mazauna yankin da su samar musu da ingantattun bayanai domin shawo kan matsalar

Tsafe, Zamfara - 'Yan sandan jihar Zamfara da wasu jami'ai daga hukumomin tsaro da suka hada da sojoji sun tsananta sintirin sama da kasa a yankin Gusau zuwa titin Tsafe zuwa Yankara dake karamar hukumar Tsafe ta jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wannan na kunshe ne a wata takarda da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau.

'Yan sanda da sojoji sun tsananta sintiri ta kasa da jiragen sama a Zamfara
'Yan sanda da sojoji sun tsananta sintiri ta kasa da jiragen sama a Zamfara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun sace mutane 50, sun kashe wasu huɗu a Zamfara

Cikakken bayanin jami'an tsaro

Akwai rahotannin sirri da suka bayyana cewa 'yan bindiga na barazanar kai hari wasu yankunan karamar hukumar Tsafe dake jihar.
Rundunar tare da hadin guiwar wasu hukumomin tsaro ballantana sojojin sun tsananta tsaro a Tsafe da kewaye domin baiwa dukiyoyi da rayuka tsaro,"'yan sandan suka ce.
Ana kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da ayyukan su.
Ana karawa da kira ga jama'ar yankunan da su samar da ingantattun bayanai ga hukumomi na ayyukan 'yan bindigan domin daukar mataki," yace.

Malami, Dingyadi, da sauran jiga-jigan da suka halarci auren 'ya'ya 10 na Wamakko

A wani labari na daban, ministan kula da harkokin 'yan sanda, Muhammadu Maigari Dingyadi, Ministan shari'a, Abubakar Malami da gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, suna daga cikin jiga-jigan da suka halarci bikin auren 'ya'ya 10 na Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a ranar Lahadi.

Daily Trust ta tattaro cewa ministocin sun wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a wurin bikin.

Kara karanta wannan

Mahaifiyar SSG na jihar Bayelsa da aka sace ta kubuta daga hannun 'yan bindiga

Sauran jiga-jigan da suka halarci bikin sun hada da tsoffin Gwamnonin Sokoto da Zamfara, Yahaya Abdulkareem da Abdulazeez Yari, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Yahya Abdullahi wanda ya wakilci shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawal da sauran 'yan majalisu.

Fittaccen attajirin mai kudi kuma dan kasuwa na jihar Katsina, Dahiru Mangal, ya halarci bikin auren a gidan tsohon gwamnan dake Gawon Nama a jihar Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel